Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Dena Amfani da Tsaffin Takardun Naira a Najeriya

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Dena Amfani da Tsaffin Takardun Naira a Najeriya

  • Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci kan bukatar da gwamnatin Tinubu ta gabatar mata na kara wa'adin amfani da tsaffin takardun naira
  • Idan ba a manta ba kotun a cikin watan Maris ta tsawaita wa'adin amfani da kudin zuwa karshen Disamba, lamarin da AGF ya nemi kari
  • A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, ta ce yanzu 'yan Najeriya za su iya ci gaba da amfani da tsaffi tare da sabbin kudin har illa-ma-shaa-Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kotun Koli ta yanke hukunci kan yiwuyar ci gaba da amfani da tsaffin takardun naira ko akasin hakan.

A ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, Kotun Kolin ta amince 'yan Najeriya su ci gaba da amfani da sabo da tsohon takardun kudin har sai baba-ta-gani.

Kara karanta wannan

Yan fansho ga Tinubu: Cire tallafin mai ya jefa mu cikin mawuyacin hali

Idan za a tuno, a watan Maris 2023, Kotun Koli ta dage wa'adin ci gaba da kashe tsaffin takardun naira zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023, The Cable ta ruwaito.

Kotun Koli/Shugaba Tinubu/Naira
Kotun Koli ta yarjewa 'yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsoho tare da sabon naira a lokaci daya.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa gwamnati ke so a kara wa'adin amfani da tsaffin kudi?

A ranar 21 ga watan Nuwamba kuwa, gwamnatin tarayya ta gabatar da wata bukata gaban Kotun Kolin na neman a kara wa'adin amfanin da tsaffin kudi.

Babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Lateef Fagbemi ne ya aike wa Kotun Koli da wannan bukata.

Fagbemi ya ce saboda matsalar tattalin arziki da ake fama da ita, gwamnati ba za ta iya buga adadin sabbin takardun naira da ake bukata kafin watan Disamba ba.

Hukuncin da Kotun Koli ta yanke

A zaman kotun da aka yi a ranar Laraba, tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin AGF, ta gabatar da bukatar karin wa'adin.

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Da yake zartar da hukuncin, kwamitin mutum bakwai karkashin jagorancin Inyang Okoro, ya ce duka tsofaffi da sabbin N200, N500 da N1000 za a ci gaba da amfani da su.

Kwamitin ya ce har sai gwamnatin tarayya ta gabatar da wani tsari bayan tuntubar masu ruwa da tsaki sannan ne za a sake duba yiyuwar daina amfani da tsaffin kudin.

Yan fansho a Najeriya sun mika bukata ga Tinubu

A wani labarin, 'yan fansho a Najeriya sun koka wa shugaban kasa Bola Tinubu kan halin da suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur, rahoton Legit Hausa.

Kungiyar 'yan fansho ta kasa (NUP) ta ce sun gabatar da bukata ga ministar jin kai don saka 'yan fansho a wani tallafin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.