Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargin Ya Saka Mata Yin Zanga-Zanga Zigidir

Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargin Ya Saka Mata Yin Zanga-Zanga Zigidir

  • Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kama wanda ake zargi da daukar nauyin matan da suka fito zanga-zanga zigidir a jihar Anambra
  • Wanda ake zargin, Ozo Jeff Nweke, a cewar rundunar 'yan sanda an kama shi ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin
  • Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wasu mata sama da dubu daya suka gudanar da zanga-zanga zigidir a Anambra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Anambra - ‘Yan sanda sun kama Ozo Jeff Nweke, wanda ake zargi da daukar nauyin matan nan da suka yi zanga-zangar zigidir a Awka, jihar Anambra.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Aderemi Adeoye, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Abuja a jiya Litinin.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi adalci, ta yanke hukunci kan mutumin da ya daɓawa maƙocinsa wuka har lahira

Rundunar 'yan sanda/Jihar Anambra
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Aderemi Adeoye, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Abuja a jiya Litinin. Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Adeoye, a wata hira da Daily Trust ta wayar tarho, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Eh Ozo Jeff Nweke an kama shi ne a Abuja.”

Ana zargin Ozo Jeff Nweke da kwacen fili

Kwamishinan ya ce ya samu koke da yawa daga al’ummomin jihar suna zargin Ozo Jeff Nweke da yin amfani da jami’an tsaron kamfanin sa na Blue Shield da ke dauke da makamai wajen kwacen filaye.

Masu zanga-zangar dai sun bukaci da a kori mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da hukumar binciken manyan laifuka ta jihar, Akin Fakorede da wani sifeta Monday Umana daga aiki.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce kafin kama Nweke a ranar Litinin, an kai kararsa a gaban kotu a Awka amma yaki halartar zaman kotun.

Mata dubu daya sun fito zanga-zanga zigidir a Anambra

A makon da ya gabata Legit Hausa ta ruwaito maku yadda sama da mata 1,000 daga kauyuka 20 a karamar hukumar Awka ta Kudu, jihar Anambra suka fito kan tituna tsirara suna zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Mata sun barke da zanga-zanga a kan tsige Gwamnan Kano a Kotu

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, inda rahotanni suka bayyana cewa, matan na zanga-zangar ne kan kashe-kashen da ake yi a garuruwansu.

Masu zanga-zangar sun bukaci a kori wasu jami'an 'yan sanda

Duk da suna tsirara ba su damu ba, haka suka karade babban birnin jihar dauke da kwalaye masu rubutu, suna zargin wasu jami'an 'yan sanda da hannu a cin hanci da rashawa.

An gansu dauke da akwatin gawa da ke nuna alamar binne jami'an 'yan sandan da suke zargi, tare da ba hukumar wa'adin kwanaki 7 ta kori jami'an.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.