Shugaba Tinubu Zai Batar da Naira Tiriliyan 27 a Kasafin Farko da Aka Yi a Zamaninsa
- Majalisar zartarwa a Najeriya (FEC) ta amince da karin da aka yi a cikin kasafin kudin da za a kashe a shekarar 2024
- Ministan kasafi ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta yi kari daga N26tr zuwa N27tr bayan sake la’akari da wasu abubuwa
- Atiku Bagudu ya tabbatar da cewa an canza hasashen farashin gangar mai da darajar Dala a kan Naira kasafin badi
Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) ta amince da N27.50tr a matsayin kasafin kudin shekarar badi da za a shiga nan da kusan kwana 30.
Premium Times ta ce an yarda da karin N1.5tr a kan lissafin farko da aka yi na kudin da gwamnatin tarayya za ta kashe a shekara mai zuwa.
An tsara kashe N26tr a MTEF
Majalisar tarayya ta amince da N26.2tr a MTEF, daga baya majalisar FEC ta yi wasu kare-kare da ya jawo kasafin ya harba zuwa N27.50tr.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan kasafi da tsare-tsaren kudi, Atiku Bagudu ya sanar da ‘yan jarida wannan a karshen taron FEC da aka yi a fadar shugaban kasa.
Da yake jawabi a birnin Abuja, Atiku Bagudu ya ce akwai bukatar karin saboda wasu canje-canje da aka samu a kasafin ma’aikatun tarayya.
Lissafin kasafin kudin gwamnati ya canza
Ministan ya ce a tsarin kashe kudin da ‘yan majalisa su ka yi na’am da shi, an yi lissafin Dala ne a N700 da farashin gangar mai a $73.96.
A zaman karshe da FEC tayi, an yanke farashin Dala zuwa N750 sannan na ganga ya dawo $77.96 lura da yadda kasuwar ta ke tafiya a yau.
Tribune ta rahoto Bagudu yana cewa an yi hakan ne saboda a maida karfi a kan wasu wurare takwas domin ganin an farfado da tattali.
Karin bayani sai Tinubu ya je majalisa
Idan Bola Tinubu ya isa majalisa da kundin kasafin, za a fahimci dalla-dallar abin da gwamnatin Najeriya za ta kashe a kan kowane bangare.
Ana sa ran gwamnati ta samu N18.32tr a matsayin kudin shiga a 2024 kamar yadda Wale Edun ya ce za a cika gibin ne daga taimakon AfdB.
Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudi
Ana da labari a ranar Larabar nan Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2024 a Abuja a gaban Sanatoci da kuma ‘Yan majalisar wakilai.
Abin da zai fi jan hankali shi ne babu ko sisi da gwamnati za ta ware domin tallafin man fetur wanda Muhammadu Buhari ya cire shi a bana.
Asali: Legit.ng