Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Kano, Bayanai Sun Fito

Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Kano, Bayanai Sun Fito

  • An samu ɓarkewar zanga-zanga a wasu sassa na birnin Kano domin nuna adawa da tsige Gwamna Abba da kotun ɗaukaka ƙara ta yi
  • Masu gudanar da zanga-zangar waɗanda suka shammaci ƴan sanda sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne na ƴan wasu mintuna
  • Gudanar da zanga-zangar lumanar na zuwa ne duk da umarnin da rundunar ƴan sandan jihar ta bayar na haramta yin zanga-zanga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Duk da hana gudanar da zanga-zanga a Kano da rundunar ƴan sandan jihar ta yi, al’ummar jihar a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu kan tsige Gwamna Abba

Sai dai masu zanga-zangar da suka shiga wasu titunan jihar sun ce jama’a sun zaɓi gwamna Abba Kabir Yusuf domin haka a bar shi ya yi mulkin jihar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Mata sun barke da zanga-zanga a kan tsige Gwamnan Kano a Kotu

An gudanar da zanga-zanga a Kano
An gudanar da zanga-zanga a Kano kan tsige Gwamna Abba Hoto: Nigeria Police Force, Abba Kabir Yusuf, Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Twitter

Me nene dalilin yin zanga-zangar?

Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar Hafiz Ibrahim ya ce sun shirya zanga-zangar ne inda suka yanke shawarar cewa ba za ta wuce wasu mintuna ba domin gudun kada jami’an tsaro su kama su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya nuna cewa an gudanar da zanga-zangar ne a lokaci guda, a kasuwar Kantin-Kwari, unguwar Hotoro da Naibawa a babban birnin jihar a tsakanin karfe 11:00 na safe zuwa 12:00 na rana kuma ba ta wuce wasu ƴan mintuna ba, rahoton The Nation ya tabbatar.

Masu zanga-zangar waɗanda suka shammaci ƴan sanda, sun gudanar da zanga-zangar lumanar ne ba tare da haifar da wata ɓarna ba, sai dai sun nuna rashin jin dadinsu, suna cewa “Abba muka zaɓa", "A bar Abba Gida ya mulke mu".

Idan dai za a iya tunawa, kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Gumel, ya yi gargaɗin cewa ba za a yi zanga-zanga kan rigingimun da ke faruwa a jihar kan shari'ar zaɓen gwamna, wanda yanzu haka yana gaban kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun fatattaki yan bindiga a jihar Arewa, sun ceto mutanen da suka sace

A cewarsa, jam’iyyun siyasar biyu wato New Nigeria People Party (NNPP) da APC sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zabe da kuma bayan zabe, cewa ba za su yi zanga-zanga ba.

Legit Hausa samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, kan zanga-zangar da aka yi, amma sai dai dawo da saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Magoya Bayan NNPP Mata Sun Dira Hedikwatar Ƴan Sanda

A wani labarin kuma, magoya bayan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun dira a hedikwatar rundunar ƴan sandan jihar Kano.

Ɗaruruwan matan da suka yi cincirindo a hedikwatar rundunar ƴan sandan, domin nuna adawa da abin da suka kira rashin adalcin hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng