"Allah Ya Kaddara Tinubu Zama Shugaban Kasa": Oba Na Benin Ya Aika da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya

"Allah Ya Kaddara Tinubu Zama Shugaban Kasa": Oba Na Benin Ya Aika da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya

  • Oba Ewuare II na Benin ya bayyana goyon bayansa ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Sarkin da ya ziyarci Legas a ƙarshen makon da ya gabata ya tabbatar da cewa Allah ne ya naɗa Tinubu a matsayin shugaban ƙasa wanda hakan ya nuna a nasarar da ya samu a zaɓe
  • Sai dai ya buƙaci ƴan Najeriya da su haɗa kai ba tare da la'akari da addininsu ko ƙabilarsu ba domin marawa gwamnatin Tinubu baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Marina, jihar Legas - Oba na Benin, Omo N’ Oba N’ Edo, Uku Akpolokpolo, Ewuare II, ya bayyana shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda Allah yake goyon baya.

Oba na Benin ya yi magana kan gwamnatin Tinubu
Oba na Benin ya ziyarci Gwamna Sanwo-Olu a Legas Hoto: @followlasg
Asali: Twitter

Oba na Benin yace Allah ya goyi bayan shugabancin Tinubu

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana dalilin da ya sanya Atiku da Peter Obi suka kasa yin nasara kan Tinubu a kotu

Sarkin ya ce Allah ne ya naɗa Tinubu ya zama shugaban Najeriya, inda ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa gwamnatinsa baya tare da zama lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oba na Benin ya lura cewa nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya nuna cewa Allah ne ya ba shi mulkin ƙasar nan, domin haka dole ne ƴan Najeriya su mara masa baya domin amfanin kowa.

Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba, yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu a gidan gwamnatin jihar legas da ke Marina.

Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da ziyarar sarkin a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Oba N’Edo Uku Akpolokpolo Ewuare II ya bayyana cewa:

“Allah ya ƙaddara cewa Tinubu zai zama shugaban Najeriya. Mu duka ɗaya ne. Ina son zaman lafiya da kwanciyar hankali. Dole ne mu zauna tare a matsayin tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Najeriya babba ce. Dole ne mu kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninmu kuma mu koyi zama tare a matsayin babban iyali ɗaya."

Oba Na Benin Ya Shawarci Ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Oba na Benin ya yi kira ga ƴan Najeriya da su haɗu su mara wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya.

Babban basaraken ya bayyana cewa babban abin da Shugaba Tinubu ya fi buƙata shi ne goyon bayan mutanen da yake jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng