Wani Gwamnan Ya Sake Fallasa Yadda Aka Kai Najeriya Gargara Kafin Zuwan Tinubu

Wani Gwamnan Ya Sake Fallasa Yadda Aka Kai Najeriya Gargara Kafin Zuwan Tinubu

  • Dapo Abiodun ya na cikin masu ra’ayin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi shugabanci a mummunan yanayi
  • Gwamnan jihar Ogun ya ce ana daf da gurganta kasar a lokacin da aka yi canjin gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • Duk da kukan da ake yi yau, Abiodun ya fadawa jama’a cewa abubuwa za su gyaru a karkashin jagorancin Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Lahadin nan, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya hira da ‘yan jarida inda ya tattauna kan sha’anin mulki da kasa.

A hirar da aka yi da shi a tashar Channels, Gwamna Dapo Abiodun ya ce an yi kaca-kaca da kasa da Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da Ganduje da gwamnoni uku, ya musu nasihar yadda zasu ɗauki talakawa

Buhari Tinubu
Shugaba Buhari Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Dapo Abiodun ya ce gwamatin Bola Ahmed Tinubu ta yi namijin kokari bayan rantsar da ita, an tunkari matsalolin da ke addabar kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An tunkari matsaloli gadan-gadan. Sun yi abin da babu wata gwamnati da ta taba yi a tarihin Najeriya.
Tinubu ya gaji gwamnatin da kusan komai ya tarbarbare. Na yi imani gwamnatin nan ta jajirce sosai.
Shugaba Tinubu ya yi abin da babu shugaban da ya taba yi, ya cire hannu a harkar mai domin ceton ‘yan Najeriya.

- Dapo Abiodun

Nan gaba za a ji dadin mulkin Tinubu

Abiodun ya na ganin cewa nan gaba mutane za su ji dadin gwamnati mai-ci, ya yi kira ga al’umma su kara hakura da mulkin Tinubu.

Punch ta ce gwamnan ya nuna dole ne sai an sha wahala kafin a kai ga shan dadi. Wannan shi ne ra'ayin har Gwamna Charles Soludo.

Kara karanta wannan

Gwamna ya tona gaskiyar halin da Buhari Ya damkawa Tinubu tattalin arzikin Najeriya

An kashe kafin zuwan Bola Tinubu?

Gwamnan na Ogun ya kara da cewa idan ba a cire tallafin fetur ba, abubuwa za su sukurkuce domin kuwa an rugurguza kasar a baya.

Bola Tinubu ya na shiga ofis bayan cikar wa’adin Muhammadu Buhari, ya cire tallafin fetur wanda ya jawo litar mai ta haura N600 a kasar.

Daga baya an daidaita farashin kudin kasar waje, hakan ya yi sanadiyyar tashin Dala.

Jigawa ta kai kuka wajen Tinubu

Ana da labari cewa Gwamnatin Jigawa ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya karasa aikin noman rani a yankin Hadejiya domin a samu abinci.

A 1980s Shehu Shagari ya fara aikin, Umar Namadi ya ce sai dai har yanzu akwai aiki a gaban gwamnatin tarayya kafin a kammala kwangilar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng