An Shiga Jimami Yayin da Kanwar Tsohon Gwamnan APC Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Najeriya

An Shiga Jimami Yayin da Kanwar Tsohon Gwamnan APC Ta Riga Mu Gidan Gaskiya a Najeriya

  • Yar uwar tsohon gwamna, Sanata Ben Ayade ta rasu a ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba bayan fama da jinya
  • Marigayiyar mai suna Ateb Janet Oniga ta kasance kanwa ga Sanata Ayade wacce ta mutu ta na da shekaru 54
  • Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Lahadi 26 ga watan Nuwamba inda ya yi mata addu’ar samun tsira

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kuros Riba – Tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya rasa kanwarsa a ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba.

Marigayiyar mai suna Ateb Janet Oniga ta kasance kanwa ga Sanata Ayade wacce ta mutu ta na da shekaru 54.

Kanwar tsohon gwamna Ben Ayade ta riga mu gidan gaskiya
Gwamnan ya sanr da mutuwar kanawr tasa a shafin Facebook. Hoto: Ben Ayade.
Asali: Depositphotos

Yaushe marigayiyar ta rasu?

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Kakakin tsohon gwamnan, Christian Ita, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi 26 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, gwamnan ya kuma sanar da labarin mutuwar a yau Lahadi a shafinsa na Facebook inda ya yi addu’ar samun tsira a gareta.

Marigayiya Janet ta rasu bayan ta yi fama da ‘yar gajeriyar jinya inda ta bar mijinta da kuma yara da dama.

Sanarwar ta ce:

“Iyalan Kakum a karamar hukumar Obudu da ke jihar Kuros Ribas na sanar da rasuwar Ateb Janet Oniga.
“Oniga ta rasu a ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba bayan fama da ‘yar gajeriyar jinya.
“Kafin rasuwarta, Janet mata ce mai tsoron ubangijinta da kula da addini da kuma kulawa da ‘yan uwanta.”

Sanarwar ta kara da cewa Janet mutum ce mai son mutane da kyakkyawan mu’amala da mutane, tabbas iyalanta za su yi kewarta, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari wasu garuruwa a arewa, sun tafka barna da kashe mutum 20

Sanata Ayade ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da lokacin bikin binneta da sauran bukukuwa.

Kotu ta yi hukunci kan zaben Kuros Ribas

A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari’ar zaben gwamnan jihar Kuros Riba.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Bassey Otu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.