An Sallami Wasu ’Yan N-Power, Ba Su Daga Cikin Wadanda Za a Biya Bashin Albashin Watanni 9
- Zubin farko (Batch A) na rusasshen shirin N-Power na gwamnatin jam’iyyar APC ya fara ne a watan Satumban 2016 kuma ya kare bayan shekaru hudu
- Zubi na biyu (Batch B) sun ci gajiyar shirin da ya tallafawa talakawa da yawa ne a tsakanin Agustan 2018 da Yuli 2020 kamar yadda aka bayyana
- Masu sai iuma zubi na uku da hudu (Batch C1 da C2) da aka dauka a cikin shekarar 2021, kuma su ne a yanzu ake kokarin sallama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja - N-Power ta ce masu cin gajiyar shirin a zubin farko da na biyu (Batch A da B) ba sa cikin shirin a halin yanzu.
Sai dai, har yanzu masu kula da shirin a gwamnatin Tinubu sun yi shuru game da makomai wadanda aka dauka a karkashin zubi na uku da hudu (Batch C1 da C2).
Yadda aka kawo karshen ‘Batch A da B’
Wani mai amfani da shafin sada zumunta na X ne ya dago bayani game da shurun da gwamnatin tarayya ta yi game da makomar wasu ‘yan N-Power da ke karskashin shirin farko da na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A martanin N-Power, tuni ai gwamnati ta salami diban farko da na biyu, don haka ba sa cikin wadanda ke cikin shirin a yanzu.
“Don Allah ku sani cewa, Batch A da B a yanzu ba sa cikin shirin.”
An rike kudin ‘yan N-Power
Ya zuwa yanzu, ‘yan Najeriya da yawa na ci gaba da jira da sa ran gwamnatin tarayya za ta sallame su komai kankantarsa.
A baya-bayan nan dai gwamnatin tarayya ta yi alkawarin biyan ‘yan N-Power kudaden da suke binta na shirin na tsawon watanni tara.
Ya zuwa yanzu dai ba a biya ba, kuma suna ci gaba da sa ran watarana za a biya su duk da har yanzu babu wasu bayanai game da biyan.
Koken matasa game da rike kudadensu
An bukaci masu cin gajiyar N-Power da su ke bin bashi su kara hakuri kan basukansu, Legit ta tattaro.
Wadanda ke bin bashin mafi yawanci 'yan rukunin 'C' ne da aka dauka a shekarar 2021 inda wasu ke bin bashi har na tsawon watanni tara.
A cikin wata sanarwa da N-Power su a fitar a shafin Twitter, sun sha alwashin kawo karshen dukkan matsalolin da ake fuskanta.
Asali: Legit.ng