An Nemi Babban Limamin Zamfara An Rasa Bayan Ya Yi Murabus

An Nemi Babban Limamin Zamfara An Rasa Bayan Ya Yi Murabus

  • Babban limamin masallacin Juma'a na Gusau GRA ya ɗauki matakin kawo zaman lafiya bayan ya yi murabus daga muƙaminsa
  • Sheikh Tukur Sani Jangebe ya sulale ya bar jihar Zamfara bayan ya miƙa takardar yin murabus ɗinsa daga limancin saboda sukar Gwamna Dauda Lawal
  • Sheikh Tukur ya bayyana cewa ya sulale ya bar jihar ne saboda dalilai na tsaro da kwantar da rikicin da kalamansa suka janyo a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Babban Limamin Masallacin Juma'a na Gusau GRA, Sheikh Tukur Sani Jangebe, wanda ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tsere daga jihar.

Sheikh Jangebe ya yi murabus daga muƙaminsa na Babban Limamin a ranar Juma'a da ta gabata biyo bayan wani faifan bidiyo da ya yaɗu inda aka gan shi yana yin Allah wadai da Gwamna Dauda Lawal tare da yabon magajinsa Bello Matawale.

Kara karanta wannan

Matawalle v Dauda: Rikicin siyasa ya sa limamin Juma’a ya bar masallaci a Zamfara

Babban limamin jihar Zamfara ya boye
Babban limamin Zamfara ya boye bayan ya yi murabus Hoto: punch.ng
Asali: UGC

Meyasa limamin ya ɓoye?

Da yake magana da jaridar The Punch ta wayar tarho, ya ce ya bar jihar ne saboda dalilai na tsaro tare da kawar da tashe-tashen hankula da kalaman nasa suka haifar a cikin faifan bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"A halin yanzu ba ni a cikin jihar Zamfara. Na yanke shawarar barin jihar ne saboda dalilai na tsaro sannan kuma na bar lamarin ya lafa."
"Kuna sane da cewa wasu ba su ji daɗin abin da na faɗa a cikin wannan faifan bidiyon ba, don haka na yanke shawarar yin murabus daga muƙamina na Babban Limamin kuma na bar jihar."

Sai dai, malamin wanda ya taɓa riƙe kujerar kwamishinan addini a jihar ya ƙi bayyana inda yake da kuma yin ƙarin bayani.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Gusau na jihar Zamfara, mai suna Jamilu Abdullahi, wanda ya goyi bayan matakin da malamin ya ɗauka na barin jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Jamilu ya bayyana cewa malamin ya yi daidai wajen barin jihar duba da cewa kalaman da ya yi, akwai waɗanda ba su ji daɗinsu ba kwata-kwata.

Ya yi nuni da cewa yadda lamuran siyasa suka koma yanzu ka iya sanya wa wasu da kalaman nasa ba su yi musu daɗi ba, farautarsa ko farautar iyalansa.

Shehu Sani Ya Magantu Kan Limamai Masu Addu'a

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan abin da ya ga mutane sun yi lokacin da limamin masallacin Juma'a ya yi addu'ar Allah tsine kan masu murɗiyar zaɓe.

Tsohon sanatan ya yi nuni da cewa ya cika da mamaki bayan da mutane suka ƙi amsawa da amin lokacin da limamin ya yi addu'ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng