Kotun Daukaka Kara Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Kan INEC Bisa Goyon Bayan PDP a Kotu
- Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta gargaɗi INEC da ta daina goyon bayan duk wata jam’iyyar siyasa a kotu, inda tace hakan na da illa
- A cewar kotun ɗaukaka ƙara, INEC ta nesanta kanta da takardar da ta sanya wa hannu tare da tabbatar da cewa aikin hukumar ya takaita ne kawai a gabatar da takardu a gaban kotu
- Kotun ta yi wannan tsokaci ne a hukuncin da ta yanke na tsige Abubakar Suleiman na jam’iyyar PDP kuma kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi a ranar Juma’a
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta caccaki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) saboda nuna ɓangaranci a wata shari’ar zaɓe.
A cewar Daily Trust, kotun ɗaukaka ƙara ta cigaba da cewa matakin da hukumar zaben ta dauka abin kunya ne ganin yadda ta nuna goyon baya ga wata jam’iyyar siyasa a wani lamari na zabe, inda ta nesanta kanta da takardun da ta rattaɓawa hannu.
Kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana rawar da INEC ta taka a rikicin zaɓe
Kotun ta koka da cewa hukumar zaɓen ta cigaba da nuna goyon baya ga wata jam'iyyar siyasa a lokacin da ya kamata ta ɗauki matakin tsaka tsaki a rikicin zaɓe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta yi gargadin cewa tilas ne INEC ta kasance ba tare da nuna son kai ba, tare da la’akari da cewa duk wani mataki da za ta ɗauka yana da alaƙa kai tsaye ga zaman lafiya da jin daɗin al'umma.
Wani ɓangare na bayanin kotun na cewa:
"Dole ne rawar da INEC ke taka wa a rikicin zaɓe ta taƙaita kawai kan gabatar da dukkanin takardun da aka yi amfani da su wajen zaɓe tare da bayyana abubuwan da aka yi amfani da su da kuma yadda aka same su."
Kotun Daukaka Kara Ta Ƴi Hukunci Kan Zaben Gwamna Sule
A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule a zaɓen gwamnan jihar Nasarawa na ranar 18 ga watan Maris.
Kotun ta jingine hukuncin da kotun zaɓe ta yi na tsige gwamnan tare da ba ɗan takarar jam'iyyar PDP nasara.
Asali: Legit.ng