Kamfanin NNPC Ya Bayyana Ranar Dakatar da Shigo da Mai Najeriya, Ya Yi Albishir Kan Matatar Kaduna
- Kamfanin mai na NNPC ya sanar da ranar dakatar da shigo da man fetur kasar zuwa watan Disamban shekarar 2024
- Ana hasashen wannan matakin zai rage farashin albarkatun mai yayin matatar Port Harcourt za ta fara aiki a watan Janairu
- Shugaban NNPC, Mele Kyari shi ya bayyana haka yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur a kasar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kamfanin mai na NNPC ya bayyana cewa zai dakatar da shigo da mai zuwa Najeriya a watan Disamban 2024.
NNPC ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 23 ga watan Nuwamba inda ya ce matatun man Najeriya za su fara aiki kafin wannan lokaci.
Yaushe matatun mai za su fara aiki?
Shugaban NNPC, Mele Kyari shi ya bayyana yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur a kasar, cewar Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Kakakin Majlisar Wakilai, Honarabul Abbas Tajudden ya samu halartar taron inda ya bukaci a saka matatun a kasuwa.
Legit ta tattaro cewa dillalan man fetur sun tabbatar da fara aiki na matatar Port Harcourt inda su ka ce za ta fara aiki a watan Janairun 2024.
Yaushe NNPC zai dakatar da shigo da mai?
Dillalan su ka ce fara aikin matatar ta Port Harcourt zai rage farashin albarkatun mai a kasar.
Kamfanin ya yi hasashen samun ribar naira tiriliyan 4.5 zuwa karshen wannan shekara ta 2023.
NNPC har ila yau, ta ce karisa aikin gyaran matatar Port Harcourt zai kare zuwa karshen Disamban wannan shekara da mu ke ciki.
Ya ce:
"Ina mai tabbatar muku da cewa zuwa karshen Disamban wannan shekara za mu fara aiki da matatar Port harcourt sai kuma matatar Warri a watan Janairu.
"Zuwa karshen 2024 matatar Kaduna za ta fara aiki yayin da za mu dakatar da shigo da mai zuwa Najeriya a karshen shekarar 2024."
Ma'aikata dubu 5 za su rasa albashin watan Disamba
A wani labarin, akalla ma'aikata dubu biyar ne ba za su samu albashin watan Disamba mai kamawa ba.
Wannan na zuwa yayin da aka samu matsaloli a takardun daukarsu aiki da kuma ranar haihuwarsu.
Asali: Legit.ng