Tashin Hankali Yayin da Sabon Rikici Ya Kaure a Wata Kasuwar Arewa, Rayuka 6 Sun Salwanta

Tashin Hankali Yayin da Sabon Rikici Ya Kaure a Wata Kasuwar Arewa, Rayuka 6 Sun Salwanta

  • Mummunan rikici ya kaure tsakanin yan kabilar Fulani da Gwarawa a kauyen Beji da ke karamar hukumar Bosso ta jihar Neja
  • Rikicin ya yi sanadiyar rasa rayuka shida, Fulani biyu da Gwarawa hudu a kasuwar Beji da ke ci duk mako
  • Rigimar ya samo asali ne daga yawan hare-haren da yan bindiga ke kai wa al'ummar yankin a yan baya-bayan nan

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Neja - Akalla rayuka shida ne suka salwanta yayin da sabon rikici ya kaure tsakanin Fulani da Gwarawa a kauyen Beji, karamar hukumar Bosso ta jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin wanda ya afku a ranar Laraba a kasuwar mako da ke ci ya haddasa tashin hankali a tsakanin mazauna garin.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

Rikicin kabilanci ya kaure a kasurwar Beji, jihar Neja
Tashin Hankali Yayin da Sabon Rikici Ya Kaure a Wata Kasuwar Arewa, Rayuka 6 Sun Salwanta Hoto: Mohammed Umar Bago
Asali: Facebook

Wannan shine karo na biyu da Fulani da yan banga ke karawa a kasuwar Beji, na farkon ya faru ne a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2023, wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka biyu da jikkata wasu mutane bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abun da ya haddasa rikicin

Wasu mazauna garin da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce hare-haren ta’addancin da ake ta kaiwa yankin tun daga watan Yulin wannan shekara shi ne ya rikida ya zama rikicin kabilanci.

Mazauna yankin sun koka kan yawan sace-sacen mutane da kashe-kashen da yan bindiga suka yi tsakanin watan Yuli da Satumba, lamarin da ya tilastawa wasunsu kwana a cikin saman silin dakunansu don tsoron kada yan bindiga su sace su ko kashe su.

Sun ce sintirin da jami’an tsaro ke yawan yi a hanyar Beji-Zungeru, ya dan sassauta lamarin a yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Babu 'yancin yin haka, malamin addini ya gargadi masu tare hanya don yin salla, an yada bidiyon

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja, Bello Mohammed Agaie, ya tabbatar da rikicin baya-bayan nan a sansanin sojin saman Najeriya dake Maikunkele a yayin wani shiri da hukumar soji ta shirya.

Ya ce gwamnatin jihar na ganawa da masu ruwa da tsaki da nufin shawo kan rikicin da ke faruwa.

Legit Hausa ta zanta da wani mazaunin garin Mekunkele da ke zuwa cin kasuwa a Beji inda ya tabbatar da lamarin.

Ya Dada ya bayyana cewa:

“Rikicin ya fara ne lokacin da wasu yan banga daga kabilar Gwari suka ga wani mai laifi a cikin kasuwar sai suka tunkare shi. Lokacin da suka tunkare shi sai zazzafan musu ya kaure a tsakaninsu wanda shine ya rikida ya zama rikici kasancewar su Fulani suna goyon bayan mutumin.
“Ana haka ne fa kowani bangare ya dauki makami har ya kai ga rasa rayuka sannan wasu sun ji rauni. Amma dai yanzu komai ya lafa.”

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari wasu garuruwa a arewa, sun tafka barna da kashe mutum 20

Yan bindiga sun farmaki al'ummar Zamfara

A wani labarin, mun ji cewa rayukan mutum biƴu sun salwanta a wani harin da ƴan bindiga ɗauke da makamai suka kai a jihar Zamfara.

Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a garin Kauran-Namoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Kauran-Namoda ta jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng