Kano: Yayin da Ake Rudanin Shari’ar Zabe, Abba Kabir Ya Sallami Ma’akata Dubu 3, Ya Bayyana Dalili
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin sallamar ma'aikata fiye da dubu uku bayan kammala bincike
- Gwamnatin har ila yau, ta dawo da wasu ma'aikata fiye da dubu tara bakin aikinsu bayan kammala tantance su.
- Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi shi ya bayyana haka a yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba a Kano
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sallami ma'akata 3,234 saboda daukar su aiki ba bisa ka'ida ba, cewar Daily Trust.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi shi ya bayyana haka a yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba a Kano.
Wane mataki gwamnan ya dauka?
Bichi ya ce wannan matakin na zuwa ne bayan bincike mai tsauri da aka yi ga ma'aikatan da gwamnatin Ganduje ta dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, gwamnatin ta dawo da wasu ma'aikata fiye da dubu tara bakin aikinsu bayan kammala tantance su, Legit ta tattaro.
Ya ce kwamitin tantance ma'aikatan ne ya kawo rahoto inda ya ba da shawarwari kuma su ka amince da shawarar.
Ma'aikata nawa aka sallama a Kano?
Ya ce:
"Kwamitin tantancewar ya mika rahotonsa ga gwamnatin jihar kuma an yi abin da ya ce bisa ga shawarwari a cikin rahoton.
"Mafi yawancin wadanda aka dauka ba sa cikin kasafin kudin 2023 kuma ba su da ra'ayin yin aikin ko kuma ba su ma cika neman aikin ba.
"Mafi yawansu ba su bi ka'idar daukar aiki ba inda aka samu wasu da takardun bogi yayin da aka dauki wasu kuma wadanda ba 'yan jihar Kano ba."
Bichi ya kara da cewa gwamnatin baya ta dauki ma'aikata kawai ba tare da duba bukatun ma'aikatu ba, ta yi haka don kara wa gwamnatinmu nauyin albashi.
Abba Kabir zai biya 'yan fansho
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya ware biliyan shida don biyan 'yan fansho a jihar.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin biyan ma'aikatan da su ka mutu yayin da su ke bakin aiki.
Asali: Legit.ng