Jihar Kano: Ganduje ya biya 'yan fansho bashin da suke bi na N2bn

Jihar Kano: Ganduje ya biya 'yan fansho bashin da suke bi na N2bn

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya saki N2bn don biyan 'yan fansho 1,313 bashin da suke bin gwamnatin jihar

- Abdulllahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa kudaden an ware su ne don biyan basussukan watan Nuwamba 2015 zuwa watan Yunin 2017

- Ganduje ya kara dacewa an kafa wai kwamitin kwararru kan fansho da zai bunkasa dokar 2006 ta 'yan fansho a jihar don duba yiyuwar sake fasalin wasu sashe sashe na dokar

Gwamnatin jihar Kano ta ware N2bn don biyan 'yan fansho 1,313 bashin da suke bin gwamnatin jihar. Idan za a iya tunawa, gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wani kwamitin mutane 8 don biyan masu bin gwamnatin jihar bashi daga 'yan fansho.

Da yake kaddamar da shirin biyan kudaden a cikin gamnatin jihar, gwamnan jihar Kano Abdulllahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa kudaden an ware su ne don biyan basussukan watan Nuwamba 2015 zuwa watan Yunin 2017, ta hanyar la'akari da rahoton da kwamitin ya gabatar.

Kwamitin wanda ya gudanar da aikinsa karkashin babbar sakatariya a ofishin shugaban ma'aikata, Hajiya Uwani Musa, wanda ya gabatar da rahotonsa na farko, da ya kunsi basussukan da 'yan fanshon ke bi na watan Nuwambar 2015 zuwa Yunin 2016, da kudinsu ya kai N2bn.

KARANTA WANNAN: 2019 kowa zai dara: Gwamnatin Buhari ta dawo da tallafin mai, ta ware N305bn

Jihar Kano: Ganduje ya biya 'yan fansho bashin da suke bi na N2bn
Jihar Kano: Ganduje ya biya 'yan fansho bashin da suke bi na N2bn
Asali: Depositphotos

Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi nuni da cewa tun bayan da gwamnatin Ganduje ta hau kan mulki, ta kashe sama da N36bn wajen biyan 'yan fansho a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta kuma biya 'yan fansho 5,858 har N9bn a fadin jihar, a matsayin wasu hakkokinsu na fansho, da suka hada da Giratuti, kudin mutuwa da kuma basukan da suka bi gwamnatin da ta shude.

Ganduje ya kara dacewa an kafa wai kwamitin kwararru kan fansho da zai bunkasa dokar 2006 ta 'yan fansho a jihar don duba yiyuwar sake fasalin wasu sashe sashe na dokar, don karfafa ayyukan asusun 'yan fansho da kuma hukumar gudanarwarta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel