Kure: Janar Din da Ya Jagoranci Dakarun da Suka Murkushe Maitatsine a Kano Ya Rasu
- Babban kwamanda janar na rundunar soji, Yerima Kure (mai ritaya) ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 84 a duniya
- Janar Yohanna Kure shi ne ya jagoranci dakarun soji wajen murkushe Maitatsine da jama'arsa a Kano a shekarar 1980 da kuma a Yola a shekarar 1982
- An haife shi ne a zuriyar Mai Sarauta Mallam Manhaik Kure da Mallama Tawok Kure a ranar 2 ga watan Afrelu, 1939 a Kurmin Musa, Kachia, jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa Allah ya yi wa Janar Yohanna Yerima Kure (mai ritaya) rasuwa yana da shekaru 84 a duniya.
Janar Yohana Kure, kafin ritayarsa ya kasance babban kwamanda janar (GOC) na rundunar soji ta 82 da ke Enugu, da kuma rundunar sashen makamai ta 2 da ke Ibadan.
Bajintar Janar Kure a aikin soja
Kure, wanda ya taba rike mukamin darakta a sashen ayyuka da tsare-tsare na rundunar soji, ya mutu a Kaduna bayan doguwar jinya, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shi ne ya jagoranci dakarun soji wajen murkushe Maitatsine da jama'arsa a Kano a shekarar 1980 da kuma a Yola a shekarar 1982.
Ya mutu ya bar matarsa, 'yan uwa, da kuma 'yaya masu yawa, har da jikoki da sauran abokan arzuka.
Yaushe za a yi jana'izar Janar Kure?
The Guardian ta ruwaito za a gudanar da jana'izar binne gawar Janar Y.Y Kure a ranar 1 ga watan Disamba, 2023 a garinsa Kurmin Musa, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.
Bidiyo: Atiku ya ziyarci makarantar da ya yi karatu a Adamawa, ya bada kyauta ga dalibai masu hazaka
Za a gudanar da wake-wake a ranar 29 ga watan Nuwamba 2023 a cocin ECWA da ke titin Lemu, Tudun Wada Kaduna, da misalin karfe 4 na yamma.
Tarihin Janar Kure a takaice
An haife shi ne a zuriyar Mai Sarauta Mallam Manhaik Kure da Mallama Tawok Kure a ranar 2 ga watan Afrelu, 1939 a Kurmin Musa, Kachia, jihar Kaduna, rahoton shafin blerf.org.
Ya yi karatu a makarantar mishan da ke Kwoi da kuma karatun elimantire a Kagoro kafin samun gurbin karatu a makarantar sakandire ta lardin Zaria wacce aka fi sani da Alhudahuda.
Matashi Kure ya shiga aikin sojan Najeriya ta hanyar babbar kwalejin horar da sojoji ta Najeriya (NDA a yanzu) a shekarar 1963 kuma an ba shi mukamin hafsa a shekarar 1964.
Kotun Daukaka Kara ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi
A wani labarin, kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, Legit Hausa ta ruwaito.
Kotun ta bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 10 da ke mazabar kakakin majalisar.
Asali: Legit.ng