Idan Ba Za Ka Iya Ba Ka Ba da Wuri, ECWA Ta Bukaci Buhari Ya Yi Murabus
- Kungiyar kiristoci ta ECWA ta bukaci shugaba Buhari ya yi murabus idan ba zai iya magance tsaro ba
- Shugabannin kungiyar sun koka kan yadda lamuran rashin tsaro ke ta'azzara a fadin kasar musamman Arewa
- ECWA ta bayyana haka ne yayin da ake jana'izar dalibar da aka kashe 'yar jami'ar GreenField ta jihar Kaduna
Shugabannin Evangelical Church Winning All (ECWA) sun nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus daga kujerarsa idan ba zai iya kawo karshen satar mutane ba, yayin da suka binne dalibar Jami’ar Greenfield da masu satar mutane suka kashe a jiya.
Duruwan mutane sun koka cikin masu makoki da suka halarci jana’izar wata dalibar jami’a, Dorathy Yohanna, a cocin ECWA Goodness, da ke Jihar Kaduna, inda malamai da dangin marigayiyar suka bukaci gwamnati da ta ceci Najeriya daga hannun 'yan ta'adda.
Mataimakin Sakatare Janar na ECWA, Rev. Samuel Atu, ya koka kan yadda gwamnatin tarayya da ta jihohi ke nade hannu yayin da kasar ke cikin tashin hankali, The Guardian ta ruwaito.
KU KARANTA: Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya
Atu, wanda ya koka kan gazawar gwamnati game da kalubalen tsaro a kasar nan, ya ce:
"Idan Buhari ba zai iya magance matsalar rashin tsaro da ke addabar al'umma ba, ya kamata ya koma gefe cikin mutuntawa."
Lamuran tsaro na ci gaba da lalacewa a Najeriya, in da jihohi da dama suke fuskantar hare-haren 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya.
KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana
Ya ce duk da cewa kira ga rabuwar kasar na iya zama da karfi, ba za a taba jinsa ba kuma zai zama tarihi nan gaba.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin wani taro a jihar Ogun inda gwamna Dapo Abiodun da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, su ma suka yi kira ga zaman lafiya, hadin kai, da kawo karshen tashin tashina a kasar.
Asali: Legit.ng