An Tsare Basarake da Wasu Mutum 14 a Gidan Yari Kan Yunkurin Kisan Kai da Kwacen Filaye a Oyo

An Tsare Basarake da Wasu Mutum 14 a Gidan Yari Kan Yunkurin Kisan Kai da Kwacen Filaye a Oyo

  • Wata babbar kotu mai zama a Ogbomoso, jihar Oyo ta garkame wani basarake da mutane uku bisa laifin kwacen fili da kuma yunkurin kasa
  • Kotun ta ce basaraken da mutanen za su zauna a gidan gyaran hali har zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba don duba yiyuwar ba da belinsu
  • Wadanda ake karar bayan zaman farko na sauraron karar, sun farmaki wanda ya shigar da karar, inda har suka kusa kashe shi a kauyen Aagba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Oyo - Babbar kotun jiha a Oyo mai zamanta a Ogbomoso, ta bayar da ajiyar mai sarautar Oloko na Oko, a karamar hukumar Surulere ta jihar.

Kara karanta wannan

Miji ya zargi surukinsa hakimi, basarake a Kano da kashe masa aure tare da yunkurin tozarta shi

Kotun ta garkame basaraken mai suna Oba Solomon Akinola tare da wasu mutane 14 a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, bisa laifin kwacen fili da yunkurin kisa.

Tawagar 'yan sanda
Kotun ta bayar da ajiyar basaraken da mutane 14 a gidan gyaran hali har zuwa mako mai zuwa don duba yiyuwar ba da belinsu Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Wadanda aka garkame tare da basarken sun hada da; Chief Sunday Aderinto, Chief Jimoh Asimiyu, Timothy Aderinto, Matthew Akintaro da kuma Rafiu Ganiu, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa kotu ta garkame basaraken da mutane 14

Sauran sun had da; Adejare Adeleru, Samson Ogunmola, Zachiaus Adeleru, Kamorudeen Ajibade, Raji Rasaq, Mutiu Arowosaye, Oyeyemi Oyelekan, Olusegun Oyelekan da Sheriff Adio.

Mai shari'a K.A Adedokun ya bayar da ajiyar su bayan da kotun ta dawo ci gaba da sauraron karar, inda lauyan jiha Mista I.O Abdulazeez ya ce mutanen sun farmaki wanda ya shigar da karar.

Jaridar Legit ta ruwaito lauyan ya shaidawa kotun cewa mutanen sun farmaki Dakta Isaac Abiodun a kauyen Aagba, lamarin da zamansu a waje zai zama barazana ga mai karar.

Kara karanta wannan

“Operation Hadarin Daji”: Dakarun sojoji sun ceto mutum 31 da aka yi Ggarkuwa da su a Arewa

Kotu ta sanya ranar duba yiyuwar ba da belin basaraken

A zaman kotun na farko da ya gudana a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, an gargadi basaraken da ya tabbatar ba a samu wani tashin hankali kan lamarin ba.

Mai shari'ar ya bayar da ajiyar wadanda ake karar a gidan gyara hali tare da dage shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba domin duba yiyuwar bayar da belinsu.

Dandazon mata fiye da 1,000 sun fito zanga-zanga zigidir a Anambra

A wani abu da ya ja hankulan mutane, Legit ta rahoto maku yadda wasu mata suka yi zanga-zanga tsirara a jihar Anambra kan kashe-kashe da ya addabi garin Awka, Legit Hausa ta ruwaito.

Masu zanga-zangar sun karade babban birnin jihar dauke da kwalaye da ke nuni da batancin ransu kan cin hanci da rashawa da ya mamaye 'yan sandan jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.