An Tafka Asara Yayin da Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Jihar Arewa

An Tafka Asara Yayin da Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Jihar Arewa

  • An samu tashin gobara a babbar kasuwar Oja Tuntun da ke cikin birnin Ilorin babban birnin jihar Kwara
  • Mummunar gobarar wacce ta laƙume shaguna 15 cikin shaguna 1,072 a kasuwar ta tashi ne a daren ranar Laraba
  • Hukumar kashe gobara ta jihar wacce jami'anta suka samu nasarar kashe na gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Wata mummunar gobara a daren Laraba, 22 ga watan Nuwamba ta ƙone babbar kasuwar Oja Tuntun da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare inda ta ƙone shagunan da ba su gaza 15 ba.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 2 muhimmai da ya kamata ku sani yayin da ake yanke hukuncin shari'ar zaben Nasarawa

Gobara ta tashi a wata kasuwa a Kwara
Wani hoton tashin gobara (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Kasuwar Oja Tuntun tana da shaguna kusan 1,072, rumfuna 984 da manyan shagunan ajiyar kaya 27.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hukumomi suka ce kan tashin gobarar?

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa ɓarnar ba ta da yawa.

Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, bai iya bayyana musabbabin tashin gobarar ba.

"Ɗaukin gaggawa cikin lokaci da jami'an hukumar kashe gobara suka kai, ya taimaka wajen tsirar da kayayyakin da kuɗaɗensu sun kai N25bn." A cewarsa.
"Har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba yayin da ake cigaba da gudanar da bincike."

Hukumar kashe gobarar ta kuma shawarci jama'a da su riƙa kashe kayayyakin wutar lantarki a gidajensu, wuraren aiki da kasuwanni domin guje wa aukuwar gobara a dalilin barin su a kunne, rahoton Gazettengr ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon kazamin hari a arewa, sun tafka ɓarna mai muni tare da kashe bayin Allah

Gwamna Abdulrazaq ya jajanta

Gwamna AbdulRaman Abdulrazaq ya ziyarci inda gobarar ta tashi a daren jiya Laraba.

Gwamnan ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, ya kuma yaba da ƙoƙarin da ƴan kwana-kwana suka yi wajen samun nasarar shawo kan lamarin.

Shi ma tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya jajantawa waɗanda gobarar ta shafa.

Gobara Ta Laƙume Shaguna a Kwara

A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta tashi a wani rukunin wasu shaguna guda takwas a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Gobarar wacce ta tashi a titin yankin Basin ta shafi shaguna shida cikin guda takwas ɗin inda ta laƙume kayayyakin miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng