Kotun Daukaka Kara Ta Magantu Kan Hukuncin Gwamnan Gwamnan Kano, Tace an Samu Kuskure a Takardar CTC

Kotun Daukaka Kara Ta Magantu Kan Hukuncin Gwamnan Gwamnan Kano, Tace an Samu Kuskure a Takardar CTC

  • Kotun Daukaka Kara ta magantu kan takarar hukuncin shari'ar gwamnan Kano da ta yanke, wanda wani sashe ya nuna akasin sakamakon hukuncin kotun
  • Wani bangare a cikin takardar ya nuna cewa kotun ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf, sabanin sanar da korarsa da kotun ta yi a ranar Juma'a
  • Sai dai babban magatakardar kotun, Umar Bangari, ya ce an samu kuskuren rubuta takardar ne, amma za a gyara idan bangarorin biyu sun bukaci hakan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Babban magatakardar Kotun Daukaka Kara, Umar Bangari ya yi kawo karshen ce-ce-kucen da ake yi kan hukuncin da kotun ta yanke kan zaben gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Sabon rikici ya barke a kotu tsakanin lauyoyin Abba da alkalan kotu kan fitar da takardun CTC

Mista Bangari ya ce abin da aka gani a takardar da ta fitar na hukuncin shari'ar kuskure ne na wallafa wanda kuma bai karyata ko sauya sakamakon da kotun ta yanke ba.

Kotun Daukaka Kara ta yi magana kan hukuncin da ta yanke a Kano
Kotun ta ce an samu kuskure wajen wallafa takardar ne, amma hakan bai rushe hukuncin da kotun ta yanke kan shari'ar gwamnan Kano ba Hoto: Abba Kabir Yusuf/Nasiru Gawuna
Asali: Facebook

TVCNews ya ruwaito cewa babban magatakardar ya ba da tabbacin cewa za a gyara kuskuren rubutun da zarar bangarorin da ke cikin lamarin sun shigar da kara a hukumance kan hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ja hankalin ‘yan jarida zuwa ga oda mai lamba 23 na doka ta 4 na Kotun Daukaka Kara wacce ta baiwa kotun ikon gyara duk wani kuskuren wallafa da kotu ko daya daga cikin masu ruwa da tsaki a lamarin suka gano.

Babban magatakardar ya bayyana cewa sabanin yadda ake yadawa, hukuncin da kotun ta yanke, kamar yadda aka bayyana a gaban kotun, yana nan daram, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Yayin da CTC ta tabbatar da nasarar Abba Kabir, NNPP ta fadi hanyar warware matsalar

Takardun CTC: Rikici ya barke a kotu tsakanin lauyoyin Abba da alkalan kotu

Rikici ya sake barkewa yayin da lauyoyin Gwamna Abba Kabir suka je daukaka kara a kotu, Legit Hausa ta ruwaito.

Layoyin gwamnan sun samu wata ‘yar hatsaniya da alkalan kotun bayan fitar da takardun CTC da ke tabbatar da nasarar Abba Kabir, Legit ta tattaro.

Mene ya jawo sabon rikicin?

Sabon rikicin ya barke ne bayan dukkan bangarorin sun ki amincewa da juna kan takardun CTC da kotun ta fitar a jiya, cewar Daily Trust.

Lauyoyin Gwamna Abba Kabir sun kai korafi na daukaka kara a Abuja inda su ke neman adalci a hukunci da aka yi a kuskure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.