“Operation Hadarin Daji”: Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutum 31 da Aka Yi Garkuwa da Su a Arewa
- Dakarun sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su bayan sun kai samame mabuyar yan ta'adda a karamar hukumar Tagaza da ke jihar Sokoto
- An tattaro cewa kasurguman yan ta’addan sun ja da baya bayan da dakarun sojojin Najeriya suka kara kaimi wajen kai harin
- An gudanar da aikin hadin guiwar ne a kauyen Alya Fulani da dajin Buani da ke jihar ta arewa maso yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Tangaza, jihar Sokoto - Dakarun hadin gwiwa na Operation HADARIN DAJI (OPHD), karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut, sun ceto wasu mutum 31 da aka yi garkuwa da su a jihar Sokoto.
A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta saki a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, ta ce dakarun sun gudanar da aikin ceton ne a karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sokoto.
An tattaro cewa dakarun sojin sun yi nasarar kakkabe kauyen Alya Fulani da dajin Buani, inda suka ceto mutum 3i1 da aka yi garkuwa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
"A wani aikin kakkaba na baya-bayan nan da dakarun OPHD suka yi a ranar 21 ga watan Nuwamban 2023 a karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sokoto, sun kakkabe kauyen Alya Fulani, dajin Buani, inda aka ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su.
"An lalata gaba daya wadannan mabuya na yan ta'adda da aka gano yayin da yan ta'addan suka yi watsi da mutanen da suka sace sannan suka tsere daga sansaninsu kafin isowar sojojin da suka kai harin."
Sojoji sun kubutar da wata mata a kauyen Goboro
Kamar yadda sanarwar ta kunsa, zazzafan harin da sojojin suka kai ne ya sa yan ta’addan suka yi watsi da mutanen da suka yi garkuwa da su sannan suka tsere daga sansanoninsu kafin isowar sojojin.
An kuma kai farmakin har zuwa kauyen Goboro, inda sojojin da karfin ikonsu suka kubutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita, lamarin da ya sa yan ta’addan suka watse cikin rudani.
Sojoji sun kai samame mabuyar miyagu
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Yamma sun halaka yan bindiga a Zamfara.
A wani samamen shara da suka kai kan yan ta'addan, dakarun sojin sun ragargaji yan bindigan tare da ceto mutane 5 da aka yi garkuwa da su a jihar.
Asali: Legit.ng