Wike Zai Fatattaki Direbobin Adaidaita a Abuja Daga Wata Mai Kamawa, Ya Fadi Dalili
- Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya ya sanar da shirinsa na hana yan adaidaita aiki a Abuja daga watan Disamba
- Ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta fara fitar da motocin bas da tasi na haya daga wata mai kamawa a kokarinta na kawo karshen matsalar "one chance" a Abuja
- Kamar yadda Wike ya bayyana, gwamnati bata dauki kowani mataki kan yan adaidaita bane tun da farko saboda babu madadinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya sanar da shirin dakatar da ayyukan yan adaidaita a Abuja daga watan Disamba mai kamawa.
Ministan ya fadi hakan ne yayin da yake sanar da shirye-shiryen gwamnati na kaddamar da sabbin motocin bas da tasi da za su dunga jigilar al'umma a babban birnin tarayyar, rahoton The Cable.
Wike, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Ribas, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga masu aikin gina gidaje a Abuja, inda ya kara da cewa wannan tsarin sufurin zai kawo karshen ayyukan yan "one chance" a babban birnin tarayyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene "one chance"?
Kalmar "once chance" ana amfani da shi ne kan ayyukan barayin direbobi ko fasinjoji na bogi da kan yaudari fasinjoji zuwa cikin ababen hawansu sannan sai su yi masu fashin kayayyakinsu.
A cewar Wike, komai ya kammala domin kaddamar da motocin bas da tasi din a wata mai kamawa.
Ya ce:
"Ina mai ba ku tabbacin cewa da zaran motocin bas da tasi din sun shiga hanya, matsalar 'yan one chance' zai zama tarihi.
"Sai dai kuma, idan ka yi kuskuren shiga tasi ko wata bas da ba namu ba, matsalarka ce."
Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ke son fatattakar adaidaita a Abuja
Da yake magana kan makomar yan adaidaita a babban birnin tarayya, tsohon gwamnan ya ce za a haramta ayyukan direbobin adaidaita da zaran motocin bas da tasi sun fara aiki.
A cewarsa, gwamnati bata dauki kowani mataki kan ayyukan yan adaidaita bane saboda babu madadinsu a hanyar.
Wike ya bayyana nasarar da ya samu
A wani labarin kuma, mun ji cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce ya tara Naira biliyan 110 ga gwamnati cikin watanni uku.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da wasu masu gina gidaje a Abuja inda ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda ake ba da takardar shaidar mallakar filaye (C of O) ta bogi, cewar rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng