Tsige Gwamnan Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Bukaci Lauyoyi Su Dawo da Takardun Hukuncin da Ta Yanke
- Ana zargin kotun ɗaukaka kara da neman lauyoyin da ke da hannu a shari’ar zaɓen gwamnan jihar Kano da su dawo da kwafin hukuncin da ta yanke domin a yi gyara
- Farfesa Chidi Odinkalu, tsohon shugaban hukumar NHRC ne ya yi wannan zargin yayin da ya yi Allah wadai da hakan
- A cikin takardun CTC da suka yaɗu, kotun ɗaukaka ƙara ta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf nasara, sannan kuma ta yi watsi da ƙarar da ya shigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
An yi zargin cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tuntuɓi lauyoyin da ke da hannu a shari’ar korar da aka yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano domin su mayar da takardun hukuncin da ta yanke (CTC) da ke tare da su.
Chidi Odinkalu, Farfesa a fannin shari'a kuma tsohon shugaban hukumar kare haƙƙin bil'adama ta kasa (NHRC) ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba.
Chidi ya ƙara da cewa kotun ɗaukaka ƙarar ta tuntuɓi lauyoyin da ke da hannu a shari'ar zaɓen gwamnan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Daily Trust, Kotun ɗaukaka ƙara ta haifar da ruɗani a hukuncin da ta yanke a lokacin da ta amince da duk buƙatun Gwamna Abba mai shigar da ƙara, tare da yin watsi da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke na tsige shi.
Ruɗani kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara na tsige gwamnan Kano
Kotun ɗaukaka ƙara ta kuma umurci wanda ake ƙara, jam’iyyar APC, da ta biya Gwamna Yusuf zunzurutun kuɗi har N1m, sannan a wani sakin layi, ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da ɗan takarar jam’iyyar NNPP ya yi saboda rashin cancanta.
Sai dai, Odinkalu a nasa martanin ya yi iƙirarin cewa hanyar da za a iya fahimtar hukuncin, shi ne kotun ɗaukaka ƙara ta sauya hukuncin bayan ta yi nazari kan ƙarar.
Ya kuma jaddada hakan ya ƙara buɗe idanun mutane kan sanin halin da ake ciki a ƙasar nan.
Wani ɓangare na saƙon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita na cewa:
"A yammacin yau na ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta buƙaci lauyoyi da su dawo da takardun hukuncin domin a yi gyara. Amma hakan bai shiga cikin tsarin dokar suɓutar baki ba, wannan cin hanci ne a ɓangaren shari'a."
Ba a Tsige Gwamna Abba Ba, Cewar Ƴan NNPP
A wani labarin kuma, wasu ƴan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun yi iƙirarin cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya nuna Gwamna Abba na nan daram a kujerarsa.
Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Isa Dederi ya bayyana cewa takardun sun nuna su ne suka yi nasara a kotun.
Asali: Legit.ng