Wike Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu da Ya Cimmawa Cikin Wata 3 a Ofis

Wike Ya Bayyana Wani Muhimmin Abu da Ya Cimmawa Cikin Wata 3 a Ofis

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana yadda cikin wata uku ya tara N110bn a FCTA
  • Ministan ya koka kan yadda aka bayar da takardun mallakar filaye (C of O) na bogi a birnin tarayya Abuja
  • Wike ya yi nuni da cewa zai kawo tsarin sanya lambar katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a jikin takardun C of O

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce ya tara Naira biliyan 110 ga gwamnati cikin watanni uku.

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da wasu masu gina gidaje a Abuja inda ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda ake ba da takardar shaidar mallakar filaye (C of O) ta bogi, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC mara lafiya ya kashe N7.3bn lokacin jinya? APC ta bayyana gaskiya

Wike ya tara N110bn a FCTA
Wike ya bayyana yadda ya tara N110bn a FCTA Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

A yayin taron, Wike ya ba da umarnin a riƙa biyan Naira miliyan 5 don samun takardun C of O.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane sauyi Wike zai kawo?

Ya bayyana cewa zai nemi izinin shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ƙara lambar katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a duk wata takardar C of O da gwamnatinsa za ta bayar.

A kalamansa:

"Na tara Naira biliyan 110 ga FCTA tun hawana ofis watanni uku da suka wuce. Ba za a ƙara yarda da bayar da fili ɗaya ga mutum uku ko fiye da haka ba."
"Idan muka yanke hukuncin da ya dace, wasu za su yi farin ciki, wasu kuma ba za su yi ba. Mun shirya don irin wannan faɗan."
"Zan nemi izinin shugaban ƙasa don haɗa kowane C of O da lambar NIN. Masu kuɗi za su yi adawa da hakan, amma duk abin da zai taimaki mutanenmu dole ne mu yi shi."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Atiku da Obi za su kayar da Tinubu a zaben 2027

An taɓa damfarar Wike a Abuja

Ya bayyana yadda a lokacin da yake gwamnan jihar Rivers wasu jami'an FCTA suka ba shi takardun C of O na bogi, inda har ya biya N57m na filayen, rahoton Businessday ya tabbatar.

Ya kuma soki yadda ake biyan Naira biliyan 8.9 a matsayin albashin ma’aikatan CTA da FCDA duk wata.

Masu gina gidaje a taron sun yi kira ga ministan da ya rage Naira miliyan 5 da ake buƙata domin mallakar C of O.

Wike Ya Caccaki Takarar Dino Melaye

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya caccaki tikitin takarar gwamna da jam'iyyar PDP ta ba Sanata Dino Melaye.

Wike ya yi nuni da cewa jam'iyyar PDP a jihar Kogi ta tafka babban kuskure na ba Dino Melaye tikitin takarar gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng