Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Wa’adin Amfani da Tsaffin Kudade, FG Ta Mika Rokonta

Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Wa’adin Amfani da Tsaffin Kudade, FG Ta Mika Rokonta

  • A karshe, rikita-rikatar wa’adin amfani da tsaffin kudade ya zo karshe bayan sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar da ake yi
  • Kotun koli ta sanya 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar shari’ar tare da yanke hukunci kan matsalar da ake ta cece-kuce a kai
  • Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan CBN ya umarci ‘yan Najeriya su ci gaba da amfani da tsaffin kudaden

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kotun koli ta sanya 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar sauraran korafin Gwamnatin Tarayya kan amfani da tsaffin kudade.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci kotun kolin ta yi gyara kan hukuncin amfani da tsaffin naira 100 da 200 da kuma 1000.

Kara karanta wannan

Hujjojin da aka samu a takardun CTC sun nuna ba a tsige Abba ba – Gwamnatin Kano

Kotun koli ta shirya yanke hukunci kan wa'adin amfani da tsaffin kudade
Kotun koli ta sanya ranar yanke hukunci kan wa'adin kudade. Hoto: CBN.
Asali: UGC

Yaushe kotun ta yi hukuncin farko?

A yayin hukuncin kotun, an sanya 31 ga watan Disamba a matsayin ranar da wa’adin amfani da tsaffin kudaden zai kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotun a ranar 3 ga watan Maris bayan dakatar da bankin CBN kan yanke ranar amfani da kudaden.

Har ila yau, an yanke hukuncin ne bayan jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara sun kalubalanci wannan tsari na wa’adin amfani da tsaffin kudaden.

Yaushe aka saka ranar yanke hukunci?

Daga bisani, wasu jihohi 13 sun goyi baya inda su ma su ke kalubalantar hukuncin amfani da tsaffin kudaden, cewar The Nigeria Lawyer.

Punch ta tattaro cewa Gwamnatin Tarayya ta bukaci kotun kolin ta da sake duba hukuncin har sai an samar da wani tsari kan amfani da kudaden.

Kara karanta wannan

Kano: Jigon NNPP ya tona asirin hanyar da APC ke bi don mayar da jihar karkashin ikonta saboda 2027

Kotun daga bisani, ta sanya 30 ga watan Nuwamban wannan shekara a matsayin ranar ci gaba da sauraran korafe-korafen, Barrister ta tattaro.

CBN ya yi umarni kan amfani da tsaffin kudade

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya, CBN ya umarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da amfani da tsaffin takardun kudade.

Bankin ya ce tsaffin takardun da sabbi duk halastattu ne wurin gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar su ka shiga tsoro bayan jita-jitar dakatar da amfani da tsaffin kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.