Shari'ar Kano: NNPP Ta Koka Kan Makarkashiyar da Aka Shirya Mata Kafin Shiga Kotun Koli

Shari'ar Kano: NNPP Ta Koka Kan Makarkashiyar da Aka Shirya Mata Kafin Shiga Kotun Koli

  • Shugaban NNPP na kasa ya fitar da jawabi cewa har yanzu ba su kai ga samun takardun hukuncin shari’ar zaben Kano ba
  • Abba Kawu Ali ya ce lauyoyin jam’iyyar sun nemi kotun daukaka kara ta ba su takardun CTC, sai dai ba su iya yin nasara ba
  • Ana bukatar takardun CTC domin jam’iyyar NNPP ta iya daukaka kara a shari’ar Abba Kabir Yusuf v Nasiru Yusuf Gawuna

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugabannin jam’iyyar NNPP na kasa, sun nuna damuwarsu kan yadda kotu ta hana su takardun shari’ar zaben gwamnan Kano.

Sakataren yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf watau Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da jawabin da ya fito daga uwar jam’iyya.

Kara karanta wannan

Kano: Jigon NNPP ya tona asirin hanyar da APC ke bi don mayar da jihar karkashin ikonta saboda 2027

NNPP.
Gwamna Abba Kabir Yusuf (NNPP) Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Shugaban PDP na rikon kwarya, Abba Kawu Ali ya ce sun yi kokarin karbar takardun CTC daga hannun kotun daukaka kara, abin ya gagara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Abba Kawu Ali yake cewa hakan ne zai taimaka masu wajen daukaka kara zuwa kotun koli domin ganin an ruguza nasarar APC.

Lokaci zai iya kurewa NNPP a Kano

"Sanannen abu ne cewa lokaci ya na da matukar muhimmanci a wajen shirya daukaka kara a irin wannan yanayi.
Za mu jaddada cewa mai shigar da kara ya na da kwanaki 14 ne kacal domin ya kammala shirye-shiryen zuwa kotu
Yanzu an ci kwanaki hudu a cikin 14, da alama tarko aka shiryawa masu kai kara.
Da gangan ake yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da lauyoyinsa wannan domin a hana yi masu adalci a kotun koli."

- Shugaban NNPP, Abba Kawu Ali

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Ba yau aka saba yi wa Abba haka a NNPP ba

The Guardian ta ce jawabin ya kunshi jefa makamancin wannan zargi ga hukuma lokacin da wani jami’i ya ce INEC ta cire hannunta a shari’ar.

Abba Kawu Ali ya ce an yi haka ne ba domin komai ba sai saboda a birkitawa NNPP lissafi bayan kotun korafin zabe ta tsige Abba Kabir Yusuf.

A karshe NNPP ta yi kira da a zauna lafiya, ta kuma roki a ba ta takardun hukuncin shari’ar.

Abin da ya sa ake so a tsige NNPP, ni - Abba

A wani rahoto da aka fitar, an fahimci Abba Kabir Yusuf ya na ganin saboda Rabiu Musa Kwankwaso ake son raba shi da kujerar gwamnan.

Gwamna Abba ya ce idan duniya ta ce ba za ta ba su wani abu ba saboda su na yi wa Kwankwaso biyayya, ba su bukatar wannan abin a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng