“Kar Wanda Ya Ajiye Mun Laya a Kotu”: An Sha Dirama Yayin da Alkali Ya Yi Gargadi da Kakkausar Murya
- Mai shari'a Hakeem Oshodi na babbar kotu a Ikeja, Lagas, ya gargadi jama'a da su daina barin layu a cikin kotunsa
- Oshodi ya ce kada a sake kuskuren barin laya a cikin kotunsa domin dai baya aiki kuma
- A cewar alkalin, an tsinci wani laya a cikin kotunsa bayan ya dage zama kan wata shari'a na kisan kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ikeja, jihar Lagos - Mai shari'a Hakeem Oshodi na babbar kotu a Ikeja, Lagas, ya yi gagarumin gargadi ga jama'a.
Kamar yadda jaridar Guardian ta rahoto, Oshodi ya yi gargadin cewa ya kamata mutane su daina ajiye masa layu a cikin kotunsa.
Ya yi wannan gargadin ne a yayin shari’ar wasu mutane biyar da ake tuhuma da laifin kisan wani Ifeanyi Etunmuse, a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kada wanda ya bar layu a cikin kotuna. Kada a sake maimaitawa. An tsinci wani laya bayan dage zaman karshe a shari'ar kisan kai."
Da yake nuni ga layan a matsayin kaya, ya ce "Kada ku bar kayanku a nan kuma. Baya aiki kuma," rahoton The Nation.
Mutane biyar da ake tuhuma; Atunrase Omolabi, Shittu Olawale, Olaide Opeifa, Olanrewaju Adebiyi wanda aka fi sani da Maja, da Jamiu Omosanya wanda aka fi sani da Orobo, an tuhume su da laifin yunkurin kisan kai da kisan Etunmuse a Western Funeral Home, Ijede Ikorodu.
An sheke wani yayin gwada maganin bindiga
A wani labarin, mun ji cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wasu mutane biyu kan zargin gwada maganin bindiga a kan wani mutum.
Marigayin Muhammad Ali mai shekaru 43 ya rasa ransa yayin da mai maganin gargajiya ke gwada maganin bindigan a kansa, cewar NewsNow.
Ali wanda ke kauyen Bursari a karamar hukumar Zaki ya tafi da mutanen hudu ne cikin daji don gwada maganin ko zai hana harsashin bindiga yi ma sa illa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Ahmed Wakil shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Talata 7 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng