Babbar magana: Duk muna daura guru da laya a jikinmu, kuma muna zuwa wajen bokaye - In ji wani dan majalisa

Babbar magana: Duk muna daura guru da laya a jikinmu, kuma muna zuwa wajen bokaye - In ji wani dan majalisa

- Wani dan majalisar jihar Legas ya tonawa 'yan siyasar kasar nan asiri, inda ya bayyana cewa dukan su matsafa ne

- Dan majalisar ya ce yanzu da za ace kowanne dan majalisa ya cire kayan shi a cikin majalisar nan da babu wanda zai tsira a cikin mu

- Dan majalisar ya kara da cewa hatta ma'aikatan gwamnati suma suna yin tsafi domin su samu ayi musu karin girma a wajen aiki

Duka muna daura guru da laya a jikin mu, hatta ma'aikatan gwamnati na yin amfani da asiri domin su samu karin girma a wajen aiki.

Wani dan majalisar jihar Legas kenan, Mr Moshood Oshun, yake bayar da bayani akan yadda duka 'yan siyasar Najeriya suke amfani da tsafi da asiri wajen biyan bukatunsu.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da ya halarta na Yarabawa jiya Alhamis, haka kuma ya nuna goyon bayan shi wajen bawa Yarabawa hotu a duk ranar 20 ga watan Agusta, domin su gabatar da wani bikin gargajiya da suke kira da 'Isese'.

KU KARANTA: Abokin kowa: 'Yan sanda sun tilasta budurwa ta nuna lasisin karenta ko su kamata

Dan majalisar ya bayyana cewa yanzu haka a majalisa da za ace kowanne dan majalisa ya tashi ya cire kayan shi, babu wanda zai sha a cikinsu. "Dukkan mu muna daura guru da laya a jikin mu.

"Duka 'yan siyasar Najeriya matsafa ne, muna amfani da bakin tsafi, kuma duk mun san inda muke zuwa idan lokacin zabe yayi domin mu samu mu lashe zabe. Kai hatta ma'aikatan gwamnati suna zuwa wajen bokaye domin su samu ayi musu karin girma a wajen aiki," in ji Oshun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng