"Kada Wani Ya Sake Ajiye Layyu a Kotu Na": Dirama Yayin da Alkali Ya Yi Gargadi Mai Zafi
- A ƙoƙarin juyar da tunanin alƙali wasu mutane a jihar Legas sun riƙa birne layu a harabar babbar kotun jihar Legas
- Alƙalin kotun ya yi gargaɗin cewa kada wanda ya kuskura ya sake birne masa layu a harabar kotunsa
- Mai shari'a Hakeem Oshodi ya yi gargaɗin ne yayin da za a cigaba da shari'ar wasu mutum biyar da ake zargi da laifin aikata kisan kai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Mai shari’a Hakeem Oshodi na wata babbar kotun da ke Ikeja ya gargadi jama’a da su daina barin layuka a harabar kotunsa.
Mai shari'a Hakeen Oshodi ya yi gargaɗin ne a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, lokacin da aka fara shari'ar wasu mutum biyar da ake tuhuma da laifin kisan wani mutum mai suna Ifeanyi Etunmuse, cewar rahoton jaridar The Punch.
"Kada wanda bar layuka a cikin kotun nan. Kada a sake maimaitawa. An samu layuka a lokacin ƙarshe da aka ɗage shari'ar kisan kan nan." A cewarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alƙalin, wanda ya kira laya a matsayin ‘kayayyaki’, ya gargaɗi mahalarta kotun: “Kada ku sake barin kayayyakin ku a nan. Sun daina yin aiki."
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da mutanen biyar da ake zargi, Atunrase Omolabi, Shittu Olawale, Olaide Opeifa, Olanrewaju Adebiyi wanda aka fi sani da Maja, da Jamiu Omosanya wanda aka fi sani da Orobo.
Ana tuhumar su ne da laifin yunƙurin kisan kai da kuma kisan wani mutum mai suna Etunmuse a gidan jana'izar Western, da ke Ijede a Ikorodu cikin jihar Legas.
Matar aure ta nema a raba ta da mijinta
A baya kun ji cewa wata matar aure Wata matar aure mai suna Hauwa Hamza ta tunkari wata babbar kotu a Kubwa, babban birnin tarayya, inda ta nemi a raba aurenta da mijinta, Yahaya Mohammed.
Matar auren ta nemi kotun da ta raba aurensu ne saboda mijin na ta baya bata kulawa kuma ko kaɗan baya ganin mutuncinta.
Kotu Ta Raba Auren Shekara 9
A wani labarin kuma, wata Wata kotun yanki da ke zama a unguwar Centre-Igboro, Ilorin, babban birnin Kwara ta raba auren da ke tsakanin Balkis Imam da Nasir Imam.
Kotun ta datse igiyoyin auren da ke tsakanin Miji da matarsa, wanda aka ɗaura bisa tsarin Musulunci bayan shekaru tara suna tare.
Asali: Legit.ng