Dama Ta Samu: Yadda ’Yan Najeriya Za Su Iya Yin Karatu Kyauta a Kasar Faransa
- Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya, ya sanar da bayar da cikakken tallafin karatu ga daliban kasar don ci gaba da karatun digiri
- Masu sha'awar neman wannan tallafin za su iya yin karatun da ya shafi ilimin sanin muhalli da kuma ilimin takaita hadurra
- Wannan damar ta hada da tallafin sufuri, alawus-alawus na wata-wata, shawarwari kan gidajen zama, kula da lafiya, kudaden biza, da kuma kudaden karatun kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Paris, Faransa - Ofishin jakadancin Faransa, ya sanar da fara karbar takardun 'yan Najeriya masu sha'awar yin karatun digiri na biyu a fannoni daban-daban na ilimi a kasar.
Legit.ng ta fahimci cewa, ana karbar takardar shaidar kammala karatun HND a shirye-shiryen da mutum zai nema.
Karatun digiri na biyu a Faransa: Tallafin karatu daga ofishin jakadanci
An bude karbar takardun neman tallafin karatun a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kuma za a rufe ranar Juma'a, 15 ga watan Disamba, 2023, rahoton Legit.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin karatun yana ba da tallafin sufuri, ba da alawus a kowane wata, yin jagora don nemo mahalli mai araha na dalibai, daukar nauyin kiwon lafiya har karewar wa'adin karatun, kudin biza, da kudin makaranta a makarantun jami'a na gwamnatin kasar.
Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da aka gani a shafin yanar gizon CampusFrance Nigeria, wata kungiya ce ta gwamnati mai kula da inganta ilimin Faransa.
Abubuwan da ake bukata don samun tallafin:
- Ka kasance dan Najeriya kuma mazauni a cikin Najeriya
- Ka kasance kana da matakin digiri na farko ko babbar diploma ta kasa (a ilimin muhalli ko takaita hadurra)
- Ka kasance ka kammala autar kasa (NYSC)
- Ka kasance dan kasa da shekaru 35
- Ka kasance ka himmatu sosai don yin karatun karatu a Faransa a shekarar ilimin Satumba/Oktoba 2024/2025
- Ba a bukatar kwarewar a harshen Faransanci idan bangaren da za a karanta ana koyar da shi da turanci
- Wadanda suka kammala digirin farko da matakin farko ko na biyu za su samu fifiko.
Me tallafin karatun zai shafa?
- Tallafin karatun zai dauke nauyin wadannan abubuwan: Daukar nauyi kiwon lafiya har zuwa lokacin kammala karatu
- Kudin biza
- Kudin makaranta a makarantun jami'a na gwamnati na kasar
- Kudin zirga-zirga
- Alawus a kowanne wata
- Jagoranci don nemo mahalli mai araha ga dalibai.
Yadda za ka nemi tallafin karatun
Yi rijista da neman tallafin ta hanyar "Etudes en France"
Kuna iya shiga shafin ta nan:
https://pastel.diplomatie.gouv.fr/etudesenfrance/dyn/public/authentification/login.html
Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba
Yayinda wasu kasashe suka yi waje da yan Najeriya, wasu na nan sun bude kofofinsu ga al’umman babbar cibiyar ta Afrika duba ga yadda suke bayar da gudunmawa wajen habbaka tattalin arzkin kasar da suke ziyarta, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng