Jerin sunaye: Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba

Jerin sunaye: Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba

- Da wuya a samu wata kasa a duniya da babu yan Najeriya da ke zama a cikinta da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasar

- Amma, wasu yan tsirarun miyagun yan Najeriya sun bata ma kasar suna inda hakan yasa sauran yan kasar ke shan wahala wajen samun biza

- Sai dai kuma, akwai wasu kasashe da dama da ke maraba da yan Najeriya a cikin yankinsu

Abu sananne ne cewa yan Najeriya na yawan tafiye-tafiye, don haka batun samun bizar fita waje a Naeriya zaune yake da kansa.

Yayinda wasu kasashe suka yi waje da yan Najeriya, wasu na nan sun bude kofofinsu ga al’umman babbar cibiyar ta Afrika duba ga yadda suke bayar da gudunmawa wajen habbaka tattalin arzkin kasar da suke ziyarta.

Wani sanannen shafin Twitter da ke mayar da hankali wajen kawo labarai masu dadi game da Naeriya ya wallafa jerin kasashe 44 da yan Najeriya za su iya kai ziyara ba tare da sun samu biza kafin tafiyarsu ba.

Jerin sunaye: Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba
Jerin sunaye: Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 4 da Shugaban ma’aikatan tsaro ya fada ma dakarun da ke fagen fama a Maiduguri

Kasashen sune:

1. Bangladesh (biza bayan an isa)

2. Barbados (biza kyauta na watanni shida)

3. Benin Republic (ba biza )

4. Burkina Faso (ba biza)

5. Burundi (biza bayan an isa na kwanaki 30)

6. Cameroon (ba biza)

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole a mika shugabancin kasa zuwa kudu a 2023, Sanata Gaya

7. Cape Verde (biza bayan an isa)

8. Chad (ba biza)

9. Comoros Island (biza bayan an isa)

10. Cote d' Ivoire (ba biza)

11. Djibouti (biza bayan an isa)

12. Dominican Republic (ba biza na kwanaki 21)

13. Fiji Island (ba biza na watanni hudu)

14. Gambia (ba biza na kwanaki 90)

15. Georgia (biza bayan an isa)

16. Ghana (ba biza)

17. Guinea (ba biza)

18. Guinea Bissau (ba biza na kwanaki 90)

19. Haiti (ba biza na kwanaki 90)

20. Iran (biza bayan an isa)

21. Kenya (biza bayan an isa na kwanaki 90)

22. Liberia (ba biza)

23. Madagascar (biza bayan an isa na kwanaki 90)

24. Maldives (biza bayan an isa na kwanaki 90)

25. Mali (ba biza)

26. Mauritania (biza bayan an isa)

27. Mauritius (ba biza na kwanaki 90)

28. Micronesia (ba biza na kwanaki 30)

30. Nauru (biza bayan an isa)

30. Nauru (biza bayan an isa)

31. Niger Republic (ba biza

32. Palau (biza bayan an isa na kwanaki 30)

33. Samoa (biza bayan an isa na kwanaki 60)

34. Senegal (ba biza)

35. Seychelles (biza bayan an isa na kwanaki 30)

36. Sierra Leone (ba biza)

37. Somalia (biza bayan an isa)

38. Sri Lanka (electronic travel authorization)

39. Tanzania (biza bayan an isa)

40. Timor-Leste (biza bayan an isa na kwanaki 30)

41. Togo (ba biza)

42. Tuvala (biza bayan an isa na kwanaki 30)

43. Uganda (biza bayan an isa)

44. Vanuatu (ba biza na kwanaki 30).

A wani labarin, Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu ya ce makiyaya daga kasashen ketare da ke zaune a dazukan jihar ne suka aikata laifuka da kai hare hare, The Punch ta ruwaito.

Akeredolu ya ce da dama cikin makiyayan da suka zo daga kasashen ketaren zaman dindindin suke yi a dazukan gwamnatin jihar kafin a bada umurnin korarsu.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar ban girma a ofishinsa da shugaban yankin na Hukumar Shige da Fice na Kasa, Dora Amahian, da ke wakiltan jihohin Oyo, Ondo, Osun da Ekiti ta kai masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel