Da Gaske ’Yan Bindiga Sun Kutsa Jami’ar Usman Dan Fodio Tare da Kai Hari? Gaskiya Ta Bayyana

Da Gaske ’Yan Bindiga Sun Kutsa Jami’ar Usman Dan Fodio Tare da Kai Hari? Gaskiya Ta Bayyana

  • An yi ta yada jita-jitar cewa ‘yan bindiga sun kai hari a Jami’ar Usman Dan Fodio inda aka hallaka mutum daya da raunata wasu
  • Hukumar makarantar ta karyata hakan inda ta ce babu wani hari da aka kai inda ta shawarci mutane da su yi watsi da labarin
  • Kakakin Jami’ar, Muhammad Isa shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Litinin 20 ga watan Nuwamba a Sokoto

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto – Hukumar makarantar Jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS) ta karyata jita-jitar cewa ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar.

Hukumar makarantar ta bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege wanda an kirkire shi ne don ta da hankulan jama’a.

Kara karanta wannan

An sake kama hatsabibin dilallin kwayoyi shekaru 7 bayan tserewarsa daga gidan yari a Abuja

Hukumar makarantar Usman Dan Fodio ta karyata jita-jitar kai hari makarantar
UDUS ta karyata labarin kai hari Jami'ar. Hoto: Legit.ng.
Asali: Twitter

Mene hukumar Jami'ar ke cewa?

Wannan na kunshe ne a cikin sata sanarwa wanda kakakin Jami’ar, Muhammad Isa ya fitar ga manema labarai a Sokoto, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammad Isa ya ce tabbas an kai hari amma a wani wuri mai nisan kilomita kadan ne daga makarantar.

Sanarwar ta ce:

“Hukumar makarantar Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto ta samu wani labarin cewa an kai hari makarantar tare da hallaka mutum daya.
“Labarin ya kuma bayyana cewa wasu da dama sun samu raunuka wanda jaridar Vanguard a ranar 18 ga watan Nuwamban 2023 ta wallafa.
“Hukumar makarantar ta ce ta so yin fatali da labarin amma ganin yadda dan jaridar ke son ba da labarin karya don batar da mutane, ya kamata mu yi magana.”

Isa ya ce gaskiyar maganan shi ne ‘yan bindigan sun kai hari a kauyen Dundayen Bakin Gulbi wanda ke da nisa da makarantar.

Kara karanta wannan

Wasu sun sace wayar tsohon minista a kotu wajen sauraron shari’ar zabe

Ya kara da cewa kai hari wannan kauye bai shi ne an kai hari cikin makarantar ba kamar yadda jaridar ta ruwaito, Leadership ta tattaro.

‘Yan bindiga sun sace matar dagaci a Zamfara

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

‘Yan bindigan sun bindige dan sanda da ke gadin gidan dagacin tare da sace matar dagacin yayin harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.