An Sake Kama Hatsabibin Dilallin Kwayoyi Shekaru 7 Bayan Tserewarsa Daga Gidan Yari a Abuja

An Sake Kama Hatsabibin Dilallin Kwayoyi Shekaru 7 Bayan Tserewarsa Daga Gidan Yari a Abuja

  • Jami'an hukumar NDLEA, sun samu nasarar cafke wani hatsabibin dillalin kwayoyi da ke gudanar da ayyukansa a babban birnin tarayya Abuja
  • Hukumar ta kuma cafke manajan dillalin kwayoyin, tare da kwato kilogiram 56.9 na tabar wiwi da kuma gram 42.7 na diazepam
  • Mai laifin, Ibrahim Momoh, wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel, shekaru bakwai da suka gabata ya tsere daga gidan yarin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun sake damke wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi a babban birnin tarayya Abuja.

Mai laifin, Ibrahim Momoh, wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel, shekaru bakwai da suka gabata ya tsere daga gidan yari bayan samunsa da laifin safarar kwayoyi, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Alkali ya umurci a bai wa Emefiele masauki a gidan yarin Kuje

Ibrahim Momoh, NDLEA
Mai laifin, Ibrahim Momoh, ya tsere daga gidan yari bayan samunsa da laifin safarar kwayoyi, shekaru bakwai da suka gabata Hoto: @ndlea.gov.ng
Asali: Twitter

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa an kama Momoh ne a wani samame da suka kai maboyar sa da ke Filin Dabo a yankin Dei-Dei a babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda NDLEA suka fara kama Ibrahim Momoh a Abuja

Jaridar The Guardian ta ruwaito Babafemi na cewa:

“An fara kama Ibrahim Momoh ne a ranar 27 ga Nuwamba, 2014 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 385.1."
"An gurfanar da shi a gaban kuliya, inda aka yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai da rabi a gidan yari a ranar 22 ga Yuli, 2015, amma a lokacin da yake zaman gidan yari a Kuje, ya tsere."
“Bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an NDLEA a ranar 20 ga Nuwamba, 2022, sun kai farmaki gidan ajiyar tsohon mai laifin, Ibrahim Momoh, tare da kama buhunan tabar wiwi 81 masu nauyin kilogiram 1,278."

Kara karanta wannan

Borno: Gobara ta yi barna a sansanin 'yan gudun hijira, mutane 2 sun mutu, gidaje 1,000 sun kone

Yadda NDLE ta kama Momoh karo na biyu

Daily Trust ta ruwaito cewa gidan ajiyar yana cikin wata gonar kiwon kaji a yankin Dei-Dei a Abuja, kuma na kama manajan Momoh mai suna Richard Forson Gordon, dan asalin kasar Ghana.

"Hukumar ta gurfanar da Gordon gaban kotun, inda aka yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan yari, tare da ayyana Momoh a matsayin 'mai laifi da ake nema ruwa a jallo'."
"A ranar 5 ga Nuwamba, 2023, hukumar jami’an NDLEA suka sake kai farmaki a maboyar Momoh da ke Filin Dabo, a unguwar Dei-Dei, Abuja, inda aka kama shi da kilogiram 56.9 na tabar wiwi da kuma gram 42.7 na Diazepam."

A cewar Babafemi.

Yan sanda sun kashe fitaccen mai garkuwa da mutane a Katsina

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta kashe wani fitaccen mai garkuwa da mutane, Nazifi Ibrahim, mai shekaru 22, a kauyen Unguwar Tsamiya da ke karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.