Rikicin yan achaba da yan kasuwa: Ministan Abuja ya yi umurnin rufe kasuwar Dei-Dei har sai baba-ta-gani

Rikicin yan achaba da yan kasuwa: Ministan Abuja ya yi umurnin rufe kasuwar Dei-Dei har sai baba-ta-gani

  • Ministan Abuja, Muhammad Bello, ya rufe kasuwar Dei-dei bayan rikicin da ya barke tsakan yan kasuwa da yan acaba a ranar Laraba
  • Ya ba da umarnin ne bayan ya jagoranci jami’an gwamanti da shugabannin tsaro a ziyarar gani da ido a yankin da rikicin ya faru
  • Ministan ya kuma umarci mazauna yankin da shugabannin kasuwar da su bincika su tsamo bata-garin da ke da hannu a rikicin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ministan babbar birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello, a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu, ya yi umurnin rufe kasuwar Dei-Dei har sai baba ta gani bayan rikicin da ya wakana tsakanin yan achaba da yan kasuwa.

Bello ya bayar da umurnin ne bayan ya kai ziyarar gani da ido a yankin da rikicin ya faru tare da kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Sunday Babaji, Daraktan DSS, da sauran hukumomin tsaro da manyan jami’an gwamnatin birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Abuja: Rayuka 5 sun salwanta a arangamar 'yan kasuwa da 'yan achaba

Rikicin yan achaba da yan kasuwa: Ministan Abuja ya yi umurnin rufe kasuwar Dei-Dei har sai baba-ta-gani
Rikicin yan achaba da yan kasuwa: Ministan Abuja ya yi umurnin rufe kasuwar Dei-Dei har sai baba-ta-gani Hoto: The Nation
Asali: UGC

Rikici ya fara a kasuwar ne lokacin da wata yar kasuwa mace ta fado daga kan babur sannan wata mota ta tawo da gudu ta murkushe ta har lahira.

Ministan ya umurci mazauna da shugabannin kasuwar da su tsamo yan iskan da suka haddasa rikicin, The Nation ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Ya zama dole mazauna yankin da ma shugabannin kasuwar su gano bata-garin da ke tsakaninsu, abin takaici ne yadda bata-garin suka yi amfani da bindiga wajen harbin mutane da ba su ji ba, ba su gani ba.
“A zahirin gaskiya, ni kaina nag a gawarwakin mutane hudu wannan abun bakin ciki ne, kuma ba za a lamunci hakan ba a Abuja.
“Mun amince tare da hukumomin tsaro cewa za a gudanar da bincike mai zurfi, kuma dole al’ummar yankin su ba da gudunmawarsu wajen samun mafita, in ba haka ba, ba za a samu zaman lafiya ba.

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

“An rufe kasuwar da kuma dakatar da hada-hadar kasuwanci a bakin hanya da suka takure hanya har sai hukuma ta kammala bincike kafin daukar mataki na gaba.”

Bello ya bayyana cewa rikicin bai shafi addini ko kabila ba, saboda mazauna yankin da lamarin ya shafa an san su da zaman lafiya a tsakaninsu, rahoton The Cable.

Ya kara da cewa:

“Wannan kawai lamari ne na yan iska da bata gari da suka dauki doka a hannunsu.”

Shugabannin kasuwar sun yi martani

Mataimakin Shugaban Kasuwar, Ifeanyi Chibata, ya shaida wa Ministan da tawagarsa cewa shaguna 45 zuwa 50 aka kona a kasuwar yayin da aka cinnawa ababen hawa 25 wuta wanda kudinsu gaba daya ya kai sama da naira biliyan daya.

Hakazalika, sakataren kungiyar masu siyar da timatir da albasa na Dei-Dei, Dahiru Mani ya bayyana cewa mutane hudu aka kashe a yayin rikicin.

Ya roki ministan da ya tabbatar da samar da sashen ‘yan sanda da isassun jami’ai a kasuwar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano

Abuja: Rayuka 5 sun salwanta a arangamar 'yan kasuwa da 'yan achaba

A baya mun ji cewa akalla rayukan wasu mutum biyar ne suka salwanta yayin da gidaje masu yawa suka kone sakamakon arangama tsakanin 'yan kasuwa da 'yan acaba a kwaryar birnin Abuja.

Wani mazaunin yankin ya sanar da Daily Trust cewa, hatsari ne ya ritsa da dan achaba wanda hakan ya janyo tarzoma a yankin.

'Yan kasuwan sun kai wa dan achaban hari bayan sun zarge shi da tukin ganganci wanda ya yi sanadin rasa rayuwar wani fasinja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel