Hadiman ’Yan Majalisar Dokokin Najeriya Sun Koka Kan Rashin Biyansu Albashin Watanni 15
- Hadiman majalisar da suka yiwa su Femi Gbajabiamila hidima sun koka kan rashin samun albashin watanni sama 15
- An bayyana yadda gwamnati da hukumar gudanarwar majalisar dokokin Najeriya suka gaza biyan albashin watannin
- Ba wannan ne karin farko da ake bayyana rashin biyan albashin ma'aikata ba a kasar nan, ana yawan samun irin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja - Hadiman 'yan majalisar tarayya dokokin Najeriya sun roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki a biya su albashinsu na watanni 15 da suke bin gudanarwar majalisar.
Hakazalika, sun yi kira ga sauran hukumomin yaki da rashawa irinsu EFCC da ICPC da su yi kokarin bincika wannan lamarin, The Nation ta ruwaito.
A bangarensu, sun yanke shawarin yin azumi da addu'o'i na musamman domin rokon Allah ya ba su nasarar samun albashinsu daga hannun gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka yiwa hidimar watanni 15
Wata sanarwar da aka fitar a ranar Juma'a mai dauke da sa hannun Sulaiman Abbas da Joseph Isa ta ce:
“Ma’aikatan da suka bar ofis a watan Yuni 2023, sun aikin Majalisar ne a watan Mayu, 2021, bayan sun yi aiki a matsayin hadiman ‘yan majalisa na tsawon shekaru biyu, sun sha fama da yunwa na tsawon watanni 15 daga cikin watanni 24 da suka yi suna hidima."
'Yan majalisar da aka yiwa hidima sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawal da kuma na majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, rahoton Punch.
Hakazalika, akwai sauran 'yan majalisar da suka shude a majalisa ta 9 da aka ce an yi musu hidimar da gudanarwar majalisar dokokin kasar bata biya ba.
An yi sallah don neman albashi a Zamfara
A wani labarin, wasu ma'aikatan gwamnatin jihar Zamfara sun gudanar da Salloli na musamman, a masallacin idin Gusau, babban birnin jihar ranar Asabar.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ma'aikatan sun taru a masallacin idin ne da misalin karfe 10 na safe, inda suka nemi Allah ya kawo mu su dauki kan kudaden albashinsu.
Ma'aikatan sun bayyana cewa, rabon da a ba su albashi tun watan Janairu, wanda hakan ya jefa su cikin halin kakanikayi.
Asali: Legit.ng