Rashin albashi mai kyau ne ke sa alkalai aikata rashawa – Majalisar dattawa

Rashin albashi mai kyau ne ke sa alkalai aikata rashawa – Majalisar dattawa

- Majalisar dattawa ta bayyana dalilin da yasa alkalai ke fada wa harkar karbar rashawa a yayin shari’a

- Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan shari’a ya ce rashin albashi mai kyau ne umul-aba’isin fadawarsu ga wannan harka

- Sanata Opeyemi Bamidele ya ce akwai bukatar duba wannan al’amari cikin gaggawa domin kawo gyara

Majalisar dattawa ta bayyana cewa rashin albashi mai kyau ne ke jefa alkalai ga fadawa harkar rashawa a yayin sauke hakokin da ya rataya a wuyansu na shari’a da adalci.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan shari’a, yancin dan adam da lamuran doka, Sanata Opeyemi Bamidele (APC Ekiti), ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin tantance alkalai takwas da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba kwanan nan.

Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa wajen daga darajar alkalan kotun daukaka kara zuwa matsayin alkalan kotun koli na Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Zuwa kotu: Hankalin Ndume ya tashi, an nemi Maina da ɗansa an rasa

Rashin albashi mai kyau ne ke sa alkalai aikata rashawa – Majalisar dattawa
Rashin albashi mai kyau ne ke sa alkalai aikata rashawa – Majalisar dattawa Hoto: The Nigeria Daily/Nigerian Scholars
Asali: UGC

Wadanda aka zaba sune Justis Lawal Garba, Arewa maso Yamma; Helen M. Ogunwumiju, Kudu maso Yamma; Addu Aboki, Arewa maso Yamma; I. M. M. Saulawa, Arewa maso Yamma.

Sai Adamu Jauro, Arewa maso Gabas; Samuel C. Oseji, Kudu maso Kudu; Tijjani Abubakar, Arewa maso Gabas da kuma Emmanuel A. Agim, Kudu maso Kudu.

Bamidele ya ce akwai bukatar a shiga lamarin halin da ake ciki a kasar game da jin dadin alkalai.

Ya ce karshen duba da aka yi wa albashi da alawus din jami’an shari’a da alkalai a Najeriya ya kasance a shekarar 2008 ta wata dokar majalisa.

“A wancan lokacin, farashin canjin naira zuwa dalar Amurka ya kasance N117 sabanin N467 da yake a yanzu. Hakan ya nuna karara cewa albashin alkalai ya tsaya cak tsawon shekaru sannan ma har yana faduwa a daraja,” in ji shi.

Ya ce a yanzu haka, albashin alkalan kotun koli a shekara yana kamawa naira miliyan 2.477; yayinda na alkalan kotun daukaka kara ya ke naira miliyan 1.995 sannan na alkalan babbar kotu ya ke naira miliyan 1.804.

KU KARANTA KUMA: Sanata Kwari ya yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, ya jinjinawa Elrufai

“Wannan rashi na albashi mai kyau ga alkalai ya nuna karara cewa ba a basu kariya daga fitinar kwadayi ba a bakin aiki,” in ji shi.

A wani labari na daban, sufetan ‘Yan sandan Najeriya na kasa, ya shigar da karar tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, a wani babban kotun tarayya da ke Abuja.

Shugaban ‘yan sandan ya na zargin tsohon gwamnan da laifuffuka uku da su ka hada da sata da kuma amfani da sunan wani wajen yaudarar mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel