Allah Ya Yiwa Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Manjo Janar Chris Alli Rasuwa

Allah Ya Yiwa Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Manjo Janar Chris Alli Rasuwa

  • Yanzu muke samun labarin rasuwar babban jigon siyasa da mulkin sojin Najeriya rasuwa bayan shafe shekaru da zaman ritaya
  • Manjo Janar Chris Alli ya kasance tsohon babban hafsun sojin Najeriya kuma tsohon gwamnan mulkin soja a kasar
  • Najeriya ta sha rashin manyan jiga-jigan da suka yi mata hidima a shekarun da take bukatar reno bayan mulkin kai

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Yanzu muke samun labarin cewa, tsohon shugaban hafsan sojin Najeriya, Manjo Janar Chris Alli (rtd), ya rasu, The Guardian ta ruwaito.

An haifi marigayin a watan Disamban 1944, ya yi ritaya daga aikin sojan Najeriya a matsayin Manjo Janar.

Ya rike mukamin babban hafsan soji daga 1993 zuwa 1994 a karkashin mulkin Janar Sani Abacha sannan ya kasance gwamnan soja a jihar Filato daga watan Agusta 1985 zuwa 1986 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, Sifeta ya kadu

Allah ya yiwa tsohon gwamnan soja
Allah ya yiwa tsohon hafsun soja rasuwa
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga ayyukansa da ya yi

Bayan shekaru da dama, an nada shi shugaban rikon kwarya na jihar Filato a lokacin da rikicin addini ya barke a jihar a shekarar 2004.

A lokacin da ya yi ritaya daga aikin soja, ya rubuta littafi mai suna: ‘The Federal Republic of Nigerian Army: The Siege of a Nation’.

Littafin ya yi tsokaci game da aikin soja da kuma yadda gudanarwarta ta kasance a tarihin Najeriya.

Ya kuma bayyana yadda aikin soja ya yi tasiri a kansa, da kuma abubuwan da ya fuskanta.

Janar Ali mamba ne na gudanarwar jaridar The Guardian kafin rasuwarsa, kamar yadda jaridar ta wallafa.

Najeriya ta sha samun rashin manyan wadanda suka yi mata hidima, musamman a cikin 'yan shekarun nan sanadiyyar tsufa da rashin lafiya.

Allah ya yiwa tsohon gwamnan soja rasuwa

Kara karanta wannan

Abubakar-Surajo Imam: Rundunar Sojin Najeriya ta samu farfesa na farko, bayanai sun fito

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ondo na mulkin soja, Manjo Janar Ekundayo Babakayode Opaleye ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a Abeokuta da ke jihar Ogun a yau Asabar 18 ga watan Nuwamba dalilin ciwon zuciya, cewar Leadership.

Opaleye shi ne ya rike mukamin gwamnan tsohuwar jihar Ondo da Ekiti a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida daga 1986 zuwa 1987.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel