Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin mulkin Abacha ya kwanta dama

Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin mulkin Abacha ya kwanta dama

  • Babban tsohon Soja kuma masoyin kwallon kafa ya rigamu gidan gaskiya
  • Iyalansa sun ce ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya
  • Gwamnatin jihar Kano ta yi jimamin mutuwar tsohon gwamnanta

Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin mulkin Soja, Dominic Oneya, ya rigamu gidan gaskiya yana mai shekara 73.

Hadimin gwamna Abdullahi Ganduje, Abubakar Aminu Ibrahim, ya bayyana haka a jawabin da ya sake ranar Alhamis.

Majiyoyi daga iyalansa sun bayyana cewa tsohon Sojan ya mutu ne a gidansa dake Agbarho karamar hukumar Effurun ta jihar Delta, rahoton Tribune.

Sun kara da cewa ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya saboda ko makon da ya gabata ya tafi Abuja.

Oneya, ya kasance gwamnan Kano tsakanin Agustan 1996 da Agustan 1998 lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.

Bayan haka kuma, ya kasance gwamnan jihar Benue tsakanin Agustan 1998 da Mayun 1999.

Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Kano ya kwanta dama
Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Kano lokacin mulkin Abacha ya kwanta dama Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Gwamna Ganduje Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Kungiyar IPOB da Yarbawa

Kara karanta wannan

Karin yan Boko Haram 19 sun mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, yace kokarin ballewa daga ƙasa ba shine hanyar warware ƙalubalen da muke fama da shi ba.

Ganduje ya faɗi haka ne a wurin wata Lakca da jam'iyyar APC ta shirya a Abuja, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Najeriya na fama da masu fafutukar ballewa daga cikinta daga kungiyar masu son kafa kasar Biyafara (IPOB) da kuma ta yarbawa "Jamhuriyar Odudua.'

Asali: Legit.ng

Online view pixel