Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Mulkin Soja Na Jihar Jigawa, Ibrahim Aliyu, Ya Rasu

Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Mulkin Soja Na Jihar Jigawa, Ibrahim Aliyu, Ya Rasu

  • Allah ya yi wa Tsohon gwamnan na mulkin soja na jihar Jigawa, Birgediya Janar Ibrahim Aliyu (mai murabus) rasuwa
  • Gwamnatin Jihar Jigawa ta bakin Habibu Nuhu Kila, hadimin gwaman jihar Muhammadu Badaru ya sanar da rasuwar
  • Gwamna Badaru ya ce rasuwar Janar Aliyu babban rashi ne ga jihar Jigawa ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta masa

Tsohon gwamnan na mulkin soja na jihar Jigawa, Birgediya Janar Ibrahim Aliyu (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a a Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Mulkin Soja Na Jihar Jigawa, Ibrahim Aliyu, Ya Rasu
Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Mulkin Soja Na Jihar Jigawa, Ibrahim Aliyu, Ya Rasu
Asali: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da Habibu Nuhu Kila, mashawarci na musamman ga gwamnan Jigawa a bagaren kafafen watsa labarai ya fitar.

Kara karanta wannan

Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP

Sanarwar ta ce:

"Mai girma Gwamna Muhammad Badaru Abubakar MON, mni, na jihar Jigawa, cikin jimami yana sanar da rasuwar tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Jigawa Birgediya Janar Ibrahim Aliyu (mai murabus) wanda ya rasu jiya Juma'a a Kaduna.
"Gwamna Badaru ya bayyana rasuwar Janar Aliyu a matsayin babban rashi ga mutane da gwamnatin Jigawa.

KU KARANTA: IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

"Ya ce marigayin Janar din ya sadaukar da rayuwarsa wurin yi wa al'umma hidima.
"Gwamna Badaru ya yi addu'ar Allah madaukakin sarki ya gafarta masa ya bawa iyalansa da mutanen jihar Jigawa hakurin jure rashinsa."

A farkon wannan watan, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci jihar Jigawa inda ya kaddamar da wani titi da aka saka wa sunan Janar Ibrahim Aliyu saboda irin gudunmawar da bayar a jihar.

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

Kara karanta wannan

IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

A wani labarin daban, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel