Yan Sanda Sun Cafke Wani 'Ƙwararren Ɓarawon Akuya' a Kaduna

Yan Sanda Sun Cafke Wani 'Ƙwararren Ɓarawon Akuya' a Kaduna

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

  • Wani matashi dan shekara 20 da aka bayyana a matsayin 'kwararren barawon akuyoyi' ya shiga hannun yan sanda a jihar Kaduna
  • Mansur Hassan, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna ya ce jami'ansu sun kama wanda ake zargin a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba
  • Kakakin yan sandan yayin sintiri yan sanda da yan bijilante suka yi karo da wanda ake zargin sanye da takunkumin fuska da makamai amma abokinsa ya tsere

Jihar Kaduna - Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani da ake zargi "ya kware" wurin satar akuyoyi a karamar hukumar Kagarko na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Mansur Hassan, ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarain Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Kaduna, cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, Sifeta ya kadu

An kama kwararren barawon akuyoyi a Kaduna
Yan sanda sun kama wani da aka ce kwararren barawon akuyoyi ne a Kaduna. Hoto: Rundunar Yan Sandan Najeriya
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Hassan, mataimakin sufritandan yan sanda, ya ce a ranar 11 ga watan Nuwamba, misalin karfe 4.30 na yamma, wata tawagar yan sanda masu saka idanu da yan bijilante, yayin sintiri suka kama wanda ake zargin dan shekara 20.

Ta ya ya yan jami'an tsaro suka kama barawon akuyan?

A cewarsa, wanda ake zargin dan asalin kauyan Igwa ne a karamar hukumar Kagarko.

Ya yi bayanin cewa wanda ake zargin yana dauke da muggan makamai da kuma takunkumin fuska wato facemask, Daily Nigerian ta rahoto.

Mista Hassan ya ce:

"Wanda ake zargin, wanda ya kware wurin satar akuyoyi, ya amsa cewa su biyu ne suka taho kauyen da nufin satar akuyoyi."

A lokacin da suka hango tawagar sintirin, dayan wanda ake zargin ya tsere, yayin da aka kama na biyun.

Kara karanta wannan

"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

Mista Hassan ya cigaba da cewa:

"Dayan wanda ake zargin ya tsere zuwa wani wurin da ba a sani ba, amma muna bin sahunsa kuma za mu kama shi."

Kakakin rundunar yan sandan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike na farko.

Ya yi kira ga al'umma su rika bai wa jami'an tsaro bayanai masu amfani kuma a kan lokaci domin kare afkuwar laifuka.

Yan sanda sun kama barawon shanu a Jigawa

A wani rahoto mai kama da wannan kun ji cewa yan sanda a jihar Jigawa sun kama wani Muktari Ibrahim da ake zargi da satar shanu a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Shiisu Lawan ya bayyana cewa sun gano wanda ake zargin ne bayan samun wasu bayanan sirri a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164