Rahoto Ya Hango Tsananin Tashin Farashin Kayayyakin Abinci a Shekarar 2024, G Dalilin da Ya Ja

Rahoto Ya Hango Tsananin Tashin Farashin Kayayyakin Abinci a Shekarar 2024, G Dalilin da Ya Ja

  • Ana hangi tashin farashin kayayyakin abinci a Najeriya a shekarar 2024 da ake shirin shiga nan da watanni biyu
  • Rahoton AFEX ya nuna cewa farashin kayayyaki zai ci gaba da hauhawa idan ba a aiwatar da manufofin da suka dace ba
  • Rahoton ya yi karin haske kan matsalolin da ke tattare da karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Ana bayyana fargabar dorewar hauhawar farashin kayan abinci, kamar yadda aka dade ana fuskanta a tsawon lokaci a Najeriya.

Wannan na zuwa ne yayin da rahoto ya bayyana yiwuwar samun tsaiko ga ga kokarin nahiyar Afirka na cimma burin kawo karshen yunwa nan da shekarar 2030.

Kara karanta wannan

Hadiman 'yan majalisar dokokin Najeriya sun koka kan rashin biyansu albashin watanni 15

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton samar da amfanin gona na 2023 wanda AFEX, fitacciyar kafar buga rahotannin kayayyaki ya wallafa a kwanan nan.

Yadda abinci zai yi tsada a 2024
Za a shiga 2024, abinci zai yi tsada, inji rahtoto | Hoto: QAssurance, AgFunder
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna manyan matsalolin da ke tattare da karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki, musamman a Najeriya.

Karancin abinci a Najeriya

Najeriya na fuskantar gagarumin gibin akalla metrik ton miliyan 5.7 na abinci, ga kuma hauhawar farashin abinci da ba a taba ganin irinsa ba da ya dara 31.52% a watan Oktoban 2023, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ruwaito.

Najeriya na fuskantar matsalar karancin abinci, kamar yadda aka nuna a kididdigar yunwa ta duniya, wadda Najeriya ke kan matsayi na 109 cikin kasashe 125.

Sakamakon binciken ya yi daidai da hasashen da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) ta yi, inda ta yi hasashen cewa nan da shekarar 2024, kusan mutane miliyan 26.5 a Najeriya za su yi fama da matsalar karancin abinci.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan Shehu Shagari tsohon shugaban kasar Najeriya

Halin da ake ciki a yanzu

A cewar jaridar The Guardian, rahoton noman amfanin gona ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman kayayyaki abinci guda shida: Masara, shinkafa, waken suya, dawa, koko, da kuma ridi.

Wadannn nau'ikan abinci dai su ne mafi yawancin abin da aka fi amfani dasu a Najeriya da ma sauran kasashen nahiyar Afrika.

Annobar Korona, yakin Rasha da Ukraine da kuma cire tallafin man fetur sun yi tasiri wajen tada farashin abinci a Afrika.

Matakin da ake dauka a Najeriya

Majalisar Wakilai a Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta kafa hukuma da za ta kayyade farashin kaya a kasar.

Wannan ya biyo bayan wani kudiri da mamban majalisar Hussaini Mohammed Jalo ya yi a jiya Alhamis 12 ga watan Oktoba.

Yayin gabatar da kudirin, dan majalisar ya ce ya kamata a dauki mataki kan tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a kasar, Daily Trust ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.