Tarihi: Yakokin Musulunci 4 da akayi cikin watan Ramadan

Tarihi: Yakokin Musulunci 4 da akayi cikin watan Ramadan

Da yawa daga cikin Musulmai basu san an yi yakoki da dama cikin watan Ramadana a zamanin sahabbai da wadanda suka biyo bayansu.

Daga yakin Fatahu Makkah zuwa yarjejeniya Baqt, da kuma yakin Badar. Amma a yau, jaridar Legit.ng zata kawo muku yakoka 4 wadanda Musulmai suka samu gagarumin nasara a cikin watan Ramadana.

1- Yakin Badar: Yakin da yafi shahara kuma yaki na faro da Musulmai sukayi a tarihi ya faru ne a watan Ramadana, shekara 2 bayan Hijran manzon Allah ﷺ daga Makkah zuwa Madina.

2-Yakin Tabuk 8 AH: Duk da cewan ba’ayi fito na fito ba wannan yaki, Musulmai sun samu gagarumin nasara yayinda rundunar 30,000 karkashin jagorancin manzon Allah ﷺ suka tafi yakan Romawa.

Amma da suka isa, aboka adawa sunyi kasa a guiwa basu fito filin daga ba.

3- Yakin Ain Jalut: An yi wannan yaki ne shekara 658 bayan hijra inda sojin Musulmi suka karfin Mongolawa da sukayi kokarin lalata kasashen Musulmai. Miliyoyin Muslmai sunyi shahada a wannan yaki.

4-Yakin Hattin: An yi wannan yaki ne a shekarar 583 bayan hijra yayinda arnan suka yai kasashen Musulmai kuma suka kwace Kudus. Bayan yakin Hattin, musulmai karkashin jagorancin Salahuddenil Ayyubi suka kwato Kudus.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel