Akwai Yiwuwar Farashin Fetur Ya Sauko, NNPCL Da Kamfanoni Sun Shigo Da Mai

Akwai Yiwuwar Farashin Fetur Ya Sauko, NNPCL Da Kamfanoni Sun Shigo Da Mai

  • ‘Yan kasuwa suna sa ran farashin da ake saida man fetur a halin yanzu ya ragu saboda shigowar kaya a makon nan
  • Manyan dillalai da kamfanin NNPCL sun shigo da gangunan mai, yanzu haka ana ta sauke kayan a tashohin ruwa
  • Masu harkar saye da saida mai sun ce karancin kaya a kasa ya na cikin abin da ya jawo hauhawar farashi a Najeriya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Farashin PMS wanda aka fi sani da man fetur zai iya saukowa a gidajen man manyan ‘yan kasuwa a makon nanda za a shiga.

Idan rahoton Punch ya tabbata, akwai yiwuwar a ga saukowar fetur bayan tashin da lita ta yi, ana kukan ya kai kusan N700 a yanzu.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi garkuwa da ni bayan tashi aiki - ‘Dan Jaridan fadar Shugaban kasa

Kamfanin NNPCL na kasa, manyan dillalai da ‘yan kasuwa sun shigo da mai sosai daga kasar waje a ranar Asabar dinnan da ta wuce.

Fetur
Fetur a gidan man NNPCL Hoto: Getty Images/Benson Ibeabuchi
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin kaya ya tashi farashin fetur

Ana tunanin karancin mai ya taimaka wajen jawo tashin farashin da ake fuskanta, idan fetur ya yalwatu, babu mamaki farashi ya karye.

Majiyoyi sun shaidawa jaridar cewa an shigo da gangunan mai da-dama ta jiragen ruwa, a jiya aka ji cewa ana sauke wasu a tashoshi.

Wasu suna ganin fetur zai iya karyewa har zuwa N300 idan aka dauki matakai.

IPMAN tana sa rai man fetur ya sauko

Sakataren yada labarai na kungiyar IPMAN ta’yan kasuwan mai masu zaman kan su, ya shaida cewa suna hangen saukowar farashin lita.

“Da zarar kayan sun fara isa gidajen mai, farashi zai ragu, saboda karancin man fetur ne ya jawo karin farashin.”

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi barna a Kaduna, sun sungume Hakimi a sababbin hare-hare

- Ukadike Chinedu

Layi da karancin fetur a gidajen mai

A ranar Alhamis, ‘yan kasuwa suka ce ba komai ya jawo ake ganin layi a gidajen mai ba illa sai saboda NNPCL kurum ke shigo da mai yanzu.

Amma kamfanin kasar ya karyata wannan batu, ya ce rikicin farashi ne na ‘yan kasuwa ya jawo ake shan wahala kafin a samu man fetur.

Nawa fetur ya ke yau a kasuwa?

A gidajen man NNPCL, ana saida litan fetur tsakanin N580 zuwa N613, amma a sauran gidajen mai da ke Najeriya farashin ya zarce haka.

Har sama da N670 ana saida lita kamar yadda mu ka ji. Da mu ka zanta da wani mai gidan mai a Kaduna, ya ce a kan N668 su ke saida litarsu.

Makonni uku da su ka wuce wani ya fada mana ya saye fetur a kan N640 a garin Minna, amma yanzu maganar da ake yi kudin ya kara tashi.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye yakin aiki, sun bada dalili

Fetur: Ina labarin matatar Dangote?

Idan abubuwa sun tafi daidai, kamfanin NNPCL zai rika saidawa Dangote danyen mai a farashin kasuwa, hakan zai kawo karshen wahalar fetur.

Ana da labari wata majiya ta ce a watan Disamban 2023, kamfanin zai warewa matatar litan danyen mai miliyan 6 domin ya fara yin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng