Yan 'Boko Haram' Sun Budewa Ayarin Motoccin Gwamna Buni Wuta, Rayuka Sun Salwanta

Yan 'Boko Haram' Sun Budewa Ayarin Motoccin Gwamna Buni Wuta, Rayuka Sun Salwanta

  • Wasu da ake zargin yan ta'addan kungiyar Boko Haram ne sun kai wa ayarin motoccin gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, hari a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kai wa tawagar gwamnan harin ne tsakanin Bensheikh zuwa Mainok
  • Yan ta'addan sun kashe jami'an yan sanda biyu sannan sun yi wa wasu yan sanda biyu rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai wa ayarin motoccin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe hari kan hanyar Maiduguri - Damaturu, inda suka kashe yan sanda biyu tare da raunata wasu biyu.

Harin ya faru ne a ranar Juma'a bayan gwamnan ya halarci taron yaye dalibai karo na 24 a Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno, rahoton Channels TV.

Yan ta'adda sun kaiwa tawagar gwamnan Yobe hari
Yan sanda biyu sun rasu a harin da yan ta'add suka kai wa ayarin motoccin Gwamna Mai Mala Buni na Yobe. Hoto: Hon Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

A kan hanyarsu ta neman mafita bayan shan kaye a zabe, 'yan jami'yya su 10 sun mutu a hatsarin mota

Yadda wadanda ake zargin yan Boko Haram din ne suka kai wa ayarin motoccin Buni hari

A cewar wani shaidan gani da ido, wanda ke cikin ayarin motoccin amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan ta'addan sun bude wa ayarin motoccin wuta ta hannu biyu na titin, suna harin jagoran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Da kyar muka tsira da ranmu yau. An kai wa ayarin motoccin hari tsakanin Beneshiekh da Mainok, kasa da kilomita shida zuwa Damaturu bayan halartar taron yaye daliban Jami'ar Maiduguri karo na 24.

"Yan ta'addan sun budewa ayarin motoccin wuta daga dukkan bangarorin titin, sun kashe dan sanda daya nan take yayin da dayan daga bisani ya rasu saboda rasa jininsa bayan harbinsa. Hasali ma, mun baro Maiduguri misalin karfe 6 na yamma."

Gwamna Buni ba ya cikin ayarin motoccin lokacin da abin ya faru a hanyarsu na komawa Damaturu babban birnin jihar. An ce ya tafi Abuja domin wani aiki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban Malami a arewa, sun kashe shi bayan karɓan kuɗin fansa

Wannan shine karon farko da aka kai wa ayarin motoccin gwamnan Yobe hari tun fara rikicin Boko Haram shekaru 12 da suka gabata.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, mai magana da yawun Gwamna Buni, Mamman Mohammed, wanda ya tabbatar da harin ya ce jami'an tsaron sunyi musayar wuta da wadanda ake zargin yan ta'addan ne.

A cewarsa:

"Sun yi harbi amma jami'an tsaron da ke ayarin gwamnan a hanyarsu na komawa Damaturu sun yi musayar wuta da su, amma yan sanda uku sun ji rauni."

Mohammed ya kara da cewa jam'ian tsaron sun yi nasarar dakile harin kuma wadanda suka jikkata suna samun sauki.

Yan Ta'adda Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Gwamna Bello Hari

A wani rahoton, gwamnatin jihar Kogi ta ce jami'an tsaro sun yi nasarar dakile wani yunkurin kisa da aka yi wa Yahaya Bello, gwamnan jihar.

Gwamnatin ta ce an farmaki gwamnan ne a jiharsa da ke tazarar kilomita kadan da birnin tarayya Abuja, kan hanyarsa na zuwa wani aiki a Lokoja, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi barna a Kaduna, sun sungume Hakimi a sababbin hare-hare

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164