“Na zata ba zai yiwu ba”: Tsoho dan shekaru 87 ya fada tarkon son kawar diyarsa, ya yi wuff da ita
- Wata mata mai shekaru 30 da ta auri tsoho dan shekaru 87 ta bayyana cewa soyayya ta gaskiya ce ta hada su
- Da take tuna baya, matar mai yara biyu ta bayyana yadda ta hadu da shi a gidan diyarsa sannan ta fada tarkon sonsa
- A nasa bangaren, mutumin ya ce bai taba yarda cewa hakan zai yiwu ba saboda mata da dama sun ki amsa tayinsa a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Winnie Mwekali Ndung'u, wata matashiyar mata ta bayyana aurenta da Ndung'u Karioki mai shekaru 92 a matsayin mai nuni ga soyayya ta gaskiya.
Ma'auratan, wadanda suka yi aure a 2014 lokacin da mutumin yake shekaru 87 sannan ita take shekaru 30, sun yi hira da Afrimax sannan suka ba da labarin yadda suka hadu.
Yadda Winnie ta hadu da Karioki
Da yake magana da yarenta, Winnie ta ce dattijon mijinta mahaifin kawarta ne. Kan yadda suka hadu, ta tuna yadda ya kawo ziyara lokacin tana a wajen kawarta kuma daga nan ne soyayya ta fara. A jawabinta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Lokacin da na hadu da wannan mutumin (Mijina), Na kasance kawar diyar mutumin nan. Na ziyarci gidan diyar.
"Yanzu, sai mutumin ya zo daga bisani a wannan rana. Lokacin da mahaifin ya zo, ya gano ni a cikin gidan diyar. Abu na farko da na gani a yanayin mahaifin, wanda yake mijina a yanzu. Ya gano ni. Na gano shi sannan muka fada tarkon so a wannan rana."
Karioki ya ce ya zata auren Winnie abu ne da ba zai yiwu ba
Dattijon ya fada ma Afrimax cewa ya shafe tsawon shekaru yana rayuwa shi kadai tun bayan mutuwar matarsa sannan ya lura cewa yana son Winnie lokacin da ya gan ta a wajen diyarsa.
"Tun daga lokacin da matata ta farko ta mutu, ni kadai nake rayuwa har sai da na hadu da yarinyar nan. Ta zo da diyata kuma kawaye ne su. Da na gane cewa ina sonta, ban yi tunanin ita ma tana jin haka game da ni ba saboda ta yi mani kankanta da yawa.
"Na zata ba zai yiwu ba saboda na tunkari sauran mata da dama inda na nemi aurensu amma suka yi watsi da ni, duba ga cewar na tsufa da yawa."
Ma'auratan sun samu yardan iyayen Winnie kuma Allah ya albarkace su da yara biyu, namiji da mace.
Matashiya ta auri dan shekaru 80
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wata mata da ta dulmiya a cikin soyayya ta baiwa mutane da dama mamaki bayan ta bayyana irin soyayyar da suke sha da sahibinta, wanda zai iya yin kaka da ita.
Matashiyar wacce ta fito daga Mudaka, yankin Kudancin Kivu a damokradiyyar Kongo, ta ce soyayya babu ruwansa da banbancin shekaru kuma bai da iyaka.
Asali: Legit.ng