Kashim Shettima Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Magance Matsalar Rashin Tsaro a Yankin Arewa Maso Gabas
- Kashim Shettima ya yi magana kan matsalar tsaron da ta daɗe tana addabar yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
- Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a iya magance matsalar ne idan masu ruwa da tsaki sun haɗa kai
- Shettima ya yi fatan cewa zaman lafiya mai ɗorewa zai dawo yankin idan aka kawar da matsalar ƴan ta'adda
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a ranar Juma’a, ya danganta wahalhalun da mazauna yankin Arewa maso Gabashin ƙasar nan ke fuskanta da ayyukan ƴan ta’adda.
Shettima, wanda ya koka kan yadda ta’addanci ya dade yana addabar yankin, ya bayyana fatansa na ganin an shawo kan wannan annoba, cewar rahoton The Punch.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna, ‘Terrorism and Counter-Terrorism in North-East Nigeria: Emerging Perspectives and the Imperative of Airpower’, a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce hanya za a kawo ƙarshen matsalar tsaron?
Shettima wanda Godswill Akpabio ya karanta jawabinsa a wajen, ya ce za a iya sake samun zaman lafiya a yankin idan duk masu ruwa da tsaki sun kuɗuri aniyar yin aiki tare.
A kalamansa:
"Yankin Arewa maso Gabas ya daɗe yana fama da matsalar ta’addanci. Mummunan ayyukan da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ke yi ya jawo wa al'ummar yankin da ba su ji ba ba su gani ba wahalhalu masu yawa."
"Amma a cikin wannan duhu, akwai fata. Fatan cewa ta hanyar ilimi, fahimta, da ƙoƙarin haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki, za mu iya shawo kan waɗannan ƙalubale da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin."
An samu cigaba wajen yaƙi da ƴan ta'adda
Babban hafsan hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana cewa tura jiragen yaƙi a yankin ya taimaka wajen murƙushe ƴan ta’adda.
Ya ƙara da cewa, tura jiragen ya ba rundunar damar gudanar da bincike da tattara bayanan sirri, tare da kai farmaki kan ƴan ta’addan.
Najeriya Na Buƙatar N21trn, Cewar Shettima
A wani labarin kuma, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar tiriliyan 21 domin magance matsalar ƙarancin gidaje.
Shettima ya kuma bayyana cewa a yanzu haka Najeriya na buƙatar ƙarin gidaje miliyan 28, a faɗin ƙasar.
Asali: Legit.ng