Tinubu: Tsofaffin Gwamnoni, Mutanen Buhari da APC Ana Kamun Kafan Neman Mukami
- ‘Yan siyasa da da-dama da ba a ba su mukamai a gwamnatin tarayya ba sun koma neman zama jakadun kasashen waje
- Akwai tsofaffin gwamnoni zuwa ministoci da su ke so Bola Ahmed Tinubu ya ba su kujerar gwamnati da za su rage zafi
- Jiga-jigai a APC da magoya bayan shugaba Tinubu sun kwallafa rai wajen zama jakadu zuwa kasashen da ake ji da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja- Tsofaffin gwamnoni, ministoci da jami’an da su ka yi aiki da Muhammadu Buhari sun dage wajen neman mukamai a gwamnati.
Punch ta ce ba su kadai ba, har da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da abokan siyasar Bola Tinubu su ke harin zama jakadu zuwa kasashen waje.
Fitattun ‘yan siyasa irinsu ‘yan majalisar tarayya da su ka rasa kujerunsu da tsofaffin manyan jami’o’in sojoji duk suna sa ran mukaman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dawo da Jakadun da ke waje
Najeriya ta na da alaka da kasashe 109, ofishin jakadanci 76 da ofisoshi barkatai a ketare, a yanzu an dawo da jakadun da ke kasashen waje.
Janye jakadun da Mai girma Bola Tinubu ya yi, ya jawo wadanda su ka taimaka masa a zabe da kuma tafiyar siyasarsa su ke son maye gurbinsu.
Gbajabiamila da Minista sun ga ta kan su
Rahoton ya ce masu sha’awar kujerun sun tasa Femi Gbajabiamila da takardunsu, ganin shi ne shugaban ma’aikatan da ke fadar Aso Rock.
Ministan harkokin kasar waje da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin ketare, Ambasada Olusola Enikanolaiye suna ganin ta kan su.
Majiyar ta ce wadanda ba a tuna da su a rabon ministoci ba su ne kan gaba wajen ganin sun tsira da kujerar jakada zuwa manyan kasashe.
Su wa ya kamata su zama Jakadu?
Farfesa Bola Akinterinwa wanda shi ne Darekta Janar na cibiyar harkokin kasashen waje ya yi kira cewa a guji maida jakada sakayyar siyasa.
Bola Akinterinwa yake cewa kyau Bola Tinubu ya dauko kwararrun masana masu ilmin huldar kasa da kasa maimakon masu burin kansu.
Ko da mutum ya zama jakada, ana da labari idan bai aiki da kyau, Tinubu zai kore shi.
Sanusi II ya yabi Gwamnan CBN
Khalifa Muhammadu Sanusi II ya soki shekaru 8 na mulkin Muhammadu Buhari, ana kuma da labari ya yabi sabon Gwamnan bankin CBN.
Masana tattalin arziki irinsu Sanusi II sun soki hanyar da aka bi wajen buga kudi barkatai da cin bashi daga CBN wanda hakan ya karya Naira.
Asali: Legit.ng