Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Birne Gawarwakin Mutane 60
- Gwamnatin Sanata Uba Sani na jihar Kaduna ta sanar da aniyarta na birne gawarwakin mutane 60 da ba a san ko su wanene ba
- Asmau Saidu Adamu, mataimakiyar shugaban sashin lafiya na karamar hukumar Kadancin Kaduna ce ta tabbatar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da ta fitar
- An rahoto cewa za a birne gawarwakin ne a makabartar Musulmai da ke hanyar Bashama a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta birne gawarwakin wasu mutane 60 da ba a san ko su wanene ba a makabartar Musulmai da ke hanyar Bashama.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, za a yi jana'izar mutanen ne a yau Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Asmau Saidu Adamu, mataimakiyar shugaban sashin lafiya na karamar hukumar Kadancin Kaduna ta fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asama'u ta bayyana cewa Mista Gabriel Brown, shugaban babban asibiti na Gwamna Awan, ne zai jagoranci birne gawarwakin, rahoton Trust Radio.
Bam ya tashi da masu zuwa jana'iza
A wani labarin, mun ji a baya cewa akalla mutanen kauye 20 ne suka rasa rayuwarsu yayin da wani babur ya tashi da bam din da kungiyar ta'addanci watau Boko Haram ta dasa a jihar Yobe.
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, abun fashewar ya tashi da mutanen ne ranar Talata da misalin ƙarfe 6:30 na yammaci.
Wannan lamari ya faru ne a ƙauyen Goni Mittiri da ke yankin garin Gumsa a ƙaramar hukumar Gaidam, jihar Yobe a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.
An tattaro cewa masu zaman makoki a kauyen mai tazarar kilomita 20 daga garin Gaidam, sun tafi jana’izar mutane 17 da harin Boko Haram ya rutsa da su lokacin da lamarin ya faru.
Yan bindiga sun afkawa masu zuwa jana'iza
Haka kuma, mun ji cewa akalla mutane fiye da 37 ne suka mutu yayin da da dama suka samu raunuka a wani harin ‘yan bindiga a jihar Sokoto.
An kai hare-haren ne a yankuna da dama a karamar hukumar Tangaza da ke jihar a ranar Asabar 3 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng