An Yi Jana'izar Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi
An gudanar da Sallar Jana'iza tare da bizne mairgayi mai martaba Sarkin masarautar Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, yau Laraba, 1 ga watan Febrairu, 2023.
Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar akwai manyan sarakunan Arewa, jiga-jiga yan siyasa, manyan malaman addini da kuma yan'uwa da abokan arziki.
Babban limamin masallacin Dutse, Sheikh Abubakar Birnin Kudu; Sheikh AbdulWahab Imamu Ahlus-Sunnah, da sauran jiga-jigan Malaman.
Hakazalika An ga mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar; tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; gwamnan jihar Jigawa, Badaru Talamiz; da mataimakinsa.
Haka akwai dan takarar gwamnan jihar Jigawa na PDP, Mustapha Sule Lamido; mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna; da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar.
![jana'iza jana'iza](https://cdn.legit.ng/images/1120/a8350e4a24fc9107.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
![Janaiza Janaiza](https://cdn.legit.ng/images/1120/9a3327e9a0f6dacd.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
![Jana'iza Jana'iza](https://cdn.legit.ng/images/1120/8fddb0321e6896dd.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
![Janaiza Janaiza](https://cdn.legit.ng/images/1120/427e61223c5a799c.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
![Janaiza Janaiza](https://cdn.legit.ng/images/1120/8258a45c7b4b569a.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
![Janaiza Janaiza](https://cdn.legit.ng/images/1120/8f4627a98471bdcc.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Asali: Legit.ng