Kotu Ta Dakatar da Gwamnan PDP Daga Sauke Shugabar Alkalan Jihar, Ta Ba Shi Umarni Mai Tsauri

Kotu Ta Dakatar da Gwamnan PDP Daga Sauke Shugabar Alkalan Jihar, Ta Ba Shi Umarni Mai Tsauri

  • Kotun masana’antu a jihar Osun ta dauki mataki kan Gwamna Ademola Adeleke kan shirin korar shugabar alkalan jihar
  • Kotun ta dakatar da gwamnan ne kan shirinsa na tuge Mai Shari’a Oyebola Ojo daga mukaminta na shugabar alkalan jihar
  • Kotun wacce ke zamanta a Ibadan babban birnin jihar ta umarci gwamnan ya kara wa Ojo jami’an tsaro don kare ta daga cin zarafi

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun – Kotun masana’antu ta Tarayya ta dakatar da Gwamna Ademola Adeleke daga daukar mataki kan shugabar alkalan jihar.

Kotun ta dauki wannan matakin ne yayin da Adeleke ke shirin sauke Mai Shari’a, Oyebola Ojo daga mukaminta, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

To fa: Gwamnan PDP ya yi watsi da umarnin Kotu, ya tsige CJ ta jiharsa ya naɗa sabo

Kotu ta dakatar da Adeleke daga korar shugabar alkalan jihar
Kotu ta yi hukunci kan shirin Adeleke na korar shugabar alkalan jihar. Hoto: Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Har ila yau, kotun ta umarci gwamnan ya kara tsaurara tsaro ga Mai Shari’a Ojo don kare ta daga duk wani cin zarafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun, Mai Shari’a, Dele Peters shi ya yi wannan hukunci a yau Alhamis 14 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke jihar.

Rahotanni sun tattaro cewa kotun ta samu korafin daga lauyan Ojo mai suna Oladipo Olasope a kan matakin gwamnan, Daily Gist ta tattaro.

Mene Ojo ke karar Gwamna Adeleke a Osun?

Ojo ta shigar da karar ce kan Gwamna Adeleke da kwamishinan shari’a da hukumar shari’a ta jihar Osun da kuma Akanta Janar na jihar.

Kotun ta shawarci kwamishina shari’a a jihar da ya bai wa wadanda ake kara shawarar bin umarnin kotun ba tare da wani tirjiya ba don samun sauki.

Bayan sauraran korafe-korafen, Mai Shari’a, Peters ya dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 12 ga watan Disamba don karisa shari’ar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano

Gwamna Adeleke ya musanta zargin matsala da Ooni na Ife

A wani labarin, gwamnatin jihar Osun ta musanta cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamna Adeleke da Ooni na Ife, Oba Ogunwusi.

An yi ta yada wani faifan bidiyo inda aka gano mai sarautar gargajiyar ya miko wa Adeleke hannu su gaisa amma ya basar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.