Bidiyo: Shin da Gaske Gwamnan PDP Ya Ki Gaisawa da Babban Basaraken Jiharsa? Gaskiya Ta Bayyana

Bidiyo: Shin da Gaske Gwamnan PDP Ya Ki Gaisawa da Babban Basaraken Jiharsa? Gaskiya Ta Bayyana

  • An yi ta yada wani faifan bidiyo inda aka gano Gwamna Adeleke na jihar Osun ya ki gaisawa da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi
  • Mutane da dama sun soki gwamnan da rashin mutunta mai sarautar gargajiya lamba daya kamar Ooni kuma mai karfin fada aji
  • Sai dai gwamnatin jihar ta yi martani inda ta tabbatar cewa an kirkiri bidiyon ne inda ta wallafa ainihin bidiyon na gaskiya

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun – An yi ta cece-kuce kan matsalar da ta taso tsakanin Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafar sadarwa, an gano dukkan masu mukamin a wurin wani taro a tare, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ba haka muka yi namu ba, Oshimole ya yi martani kan tsarin NLC, ya ba ta shawara

An bayyana gaskiyar kin gaisawa da Gwamna Adeleke ya yi da Ooni na Ife
Gaskiya ta bayyana kan zargin basar da Ooni na Ife da Adeleke ya yi. Hoto: Ademola Adeleke/ Ooni of Ife.
Asali: Facebook

Mene ake yadawa kan rashin jituwarsu?

An yanko wani bangare na bidiyon inda Gwamna Adeleke ya yi biris tare da kin gaisawa da Ooni na Ife wanda hakan ya kawo cece-kuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun caccaki gwamna da aikata haka ga babban basarake lamba daya a jihar kuma mai karfin fada aji a yankin Yarbawa.

Sai dai kuma, Gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa kan bidiyon inda ta tabbatar da cewa kirkirarshi aka yi don bata tsakaninsu, cewar Osun Defender.

Wane martani gwamnatin Osun ta yi?

A cikin sanarwar da aka fitar a yau Laraba 15 ga watan Nuwamba, an tabbatar da cewa Adeleke da Ogunwusi su na da kyakkyawar alaka a tsakaninsu.

Sanarwar ta ce:

“Gwamna Ademola Adeleke da Ooni na Ife, Ogunwusi Adeyeye su na da kyakkyawar alaka kamar yadda ake ganinsu cikin farin ciki a yayin taron.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bada mamaki, ya kai ziyarar bazata Asibitin da aka kwantar da babban jigo

“Mu na rokon jama’a da su yi watsi da wannan kirkirarren faifan bidiyo da ake yada wa a kafofin sadarwa yayin da muka wallafa na ainihi.”

Gwamna Adeleke na cikin matsala a Osun

A wani labarin, Gwamna Ademola Adeleke na cikin matsala kan korar wasu daga cikin mukarrabansa.

An maka Adeleke a kotu kan zargin rushe Majalisar gudanarwa na wasu kananan hukumomi a jihar bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan ya kori mambobin Majalisar guda hudu da tsohuwar gwamnati ta nada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel